Auren 'yar Sarkin Musulmi: Jirage 17 sun sauka a jihar Sakkwato
Babban sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha, da kuma shugaban ma'aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, sun kasance cikin dandazon manyan baki da suka halarci daurin auren Fatima Abubakar, 'yar sarkin musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III a birnin Shehu.
Amaryar Fatima, an kulla mata igiyar aure a kan sadaki na N50,000 tare da angonta, Mahmud Yuguda, dan tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata, jirage kimanin 17 dauke da manyan baki sun sauka a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Sultan Abubakar III da ke jihar Sakkwato.
An ruwaito cewa, Abba Kyari da sakataren gwamnatin kasar sun wakilci shugaban kasa Buhari a yayin babban taron na daurin aure da aka gudanar a masallacin Sultan Bello, karkashin jagorancin babban limamin jihar, Malami Akwara, yayin da Alkalin Alkalan Najeriya, Muhammad Tanko, ya gabatar da addu'o'i da kuma limamin babban masallacin Abuja, Shehu Galadanchi.
Sarkin Gwandu Muhammad Bashar, shi ne ya kasance alwalin amarya, yayin da Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu ya zamto waliyyin ango.
Cikin jerin manyan baki da suka albarkaci taron na daurin aure sun hadar da hamshakan 'yan kasuwar nan, Aliko Dangote da Dahiru Mangal.
Sauran manyan baki mahalarta daurin auren sun hadar da sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu, babban akantan kasa, Ahmed Idris, tsohon gwamnan Bauchi, Adamu Mu'azu, tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa.
KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun yi wa mutane 12 yankan rago a Nijar
Kazalika sauran manyan bakin sun hadar da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Mutawalle, gwamnan Filato, Simon Bako Lalung, gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, gwamnan Ogun, Dapo Abiodun da sauransu.
Manyan Sarakuna da suka halarci daurin auren sun hadar da mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II tare da sarakunan Maradun, Argungu da sauransu.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng