Dasuki ya sha kaye a kotun zaben jihar Sokoto

Dasuki ya sha kaye a kotun zaben jihar Sokoto

Kotun sauraron kararrakin zabe na gwamna, majalisar dokokin tarayya da na jiha a Sokoto, ta yi watsi da karar Mista Abdussamad Dasuki da ke kalubalantar nasarar zaben mamba mai ci, Alhaji Bala Kokani.

Kokani na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ya kayar da Dasuki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 na dan majalisar tarayy mai wakiltan mazabar Kebbe/Tambuwal da ke jihar Sokoto.

Dasuki ta hannun lauyansa Dr Garba Tetengi (SAN), ya jagoranci shaidu shida doin tabbatar da zargin cewa any magudin zabe, razana masu zabe, rikici, da kuma kin bin ka'idar dokar zabe.

Lauyan Kokani, Mista Solomon Alimasunya, da na APC, Mista Nuhu Adamu sun jagoranci shaida guda sannan sun karyata zarge-zargen a madadin wand ake kara.

Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, ga watan Satumba, a Sokoto, shugaban kotun zaben, Justs Yusuf Muhammad-Ubale yacemai karar ya gaza tabbatar da kararsa ta yadda hukunci zai tabbatar da shi.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Yan bindiga sun gabatar da babban bukata da suke so a cika masu kafin su ajiye makamansu

Muhammad-Ubale yace shaidun da mai karar ya gabatar sun gaza jawabin abubuwan da suka faru a lokacin da suke bayar da shaida.

Yace mutumin da ya kasance a wurin da lamarin ya afku ne ya kamata ya yi jagoranci wajen bayar da shaida wanda a wannan shari'a mai kara ya gaatar da shaidu da suka "suka ji ance".

Don haka alkalin ya kori shari'an ba tare da anci tarar kowace jam'iya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng