Kalli Amina Yahaya, shugabar dalibai ta farko mace a jami’ar Usman Danfodiyo

Kalli Amina Yahaya, shugabar dalibai ta farko mace a jami’ar Usman Danfodiyo

Wata matashiya yar Najeriya ta kafa tarihi kwanan nan yayinda ta zama shugabar kungiyar dalibai ta farko mace a wani makarantar jami’a da ke yankin arewacin kasar.

A bisa rahotanni daga WomenAfrica.com, dalibar mai suna Amina Yahaya ta zama shugabar kungiyar dalibai a jami’ar Usman Danfodio, Sokoto, wanda hakan yasa ta zamo mace ta farko da ta kai ga hawa wannan mataki tsawon shekaru masu yawa.

A baya dai Amina ta kasance tana rike da mukamin mataimakiyar Shugaban kungiyar, kafin a tsige Shugaban kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya gana da sarakunan kudu maso yamma a fadar shugaban kasa

A kuma tattaro cewa shugabar daliban a wata hira da shafin BBC Hausa, ta bayana cewa farfesa mace guda daya da suke da ita a bangaren da take ce uwargijiyarta.

Kalli hotonta a kasa:

Kalli Amina Yahaya, shugabar dalibai ta farko mace a jami’ar Usman Danfodiyo
Kalli Amina Yahaya, shugabar dalibai ta farko mace a jami’ar Usman Danfodiyo
Asali: UGC

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa yayin da a ke ta faman tafka muhawara a game da takardun karatun shugaba Muhammadu Buhari, hukumar WAEC ta hallara gaban kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa na 2019.

Henry Adeuwumi wanda babban jami’i ne na hukumar jarrabawar kammala Sakandaren makarantun kasashen Afrika ta yamma, ya tabbatar da cewa Muhammadu Buhari ya zana jarrabawar.

A cewar Henry Adewumi, shugaban na Najeriya ya yi wannan jarrabawa ne a shekarar 1961 inda ya samu shaidar Cambridge University West African Examination certificate inda ya ci kwas guda 5.

Adewumi ya bayyana wannan ne a lokacin da ya bayyana a gaban Alkalan da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa na 2019, kamar yadda mu ka samu rahoto daga hukumar dillacin labarai na kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng