Jihar Sokoto
Jami'an NDLEA sun yi nasarar kama wani mutum, Anas Sani, da ake zargin manomin ganyen wiwi ne a garin Sanyinna da ke karamar hukumar Tambuwal a jihar Sokoto.
Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Ahmed Aliyu, ɗan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Sokoto da aka yi a watan Maris.
Gwamnatin jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta bayar da umarnin sake gyara gidan tsohon shugaban ƙasa Shehu Shagari da gobara ta ƙona.
Fasto Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewa 'yan Najeriya na damunsa don ya tsaya neman takarar shugaban kasa inda su ka ce har kudin fom za su biya.
Aikin ceto da dakarun sojoji karkashin jagorancin Manjo Janar Godwin Mutkut suka yi a jihar Sokoto ya yi sanadiyar ceto mutum 31 da aka yi garkuwa da su.
Hukumar makarantar Jami'ar Usman Dan Fodio ta karyata jita-jitar cewa 'yan bindiga sun kai hari cikin makarantar tare da hallaka wani mutum daya.
Gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari da ke ungiwar Gobirawa a jihar Sokoto. An yi asarar kayayyaki masu muhimmanci a gobarar.
An samu asarar ran mutum ɗaya yayin da wasu matasa da ƴan bindiga suka yi artabu a Sokoto. Matasan dai sun tunkari ƴan bindigan ne bayan sun yi yunƙurin kawo hari.
An rasa rayuka da dama da kuma dukiyoyi bayan haddasa fada da 'yan bindiga suka yi a tsakanin kauyuka da dama a karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.
Jihar Sokoto
Samu kari