Yan bindiga sun kashe mutum 12 a sabbin hare-hare da suka kai garuruwan Kaduna da Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutum 12 a sabbin hare-hare da suka kai garuruwan Kaduna da Sokoto

- Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-hare da aka kai wasu jihohin arewa guda biyu

- Abubuwan na bakin ciki sun faru ne a Kaduna da Sokoto a ranar Laraba, 24 ga watan Maris

- Wasu da ake zargin 'yan fashi ne suna ta addabar yankunan arewa da dama a cikin yan kwanakin nan

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa an kashe Mai gari da wasu mutane 11 a hare-haren ’yan bindiga a kan garuruwa a jihohin Sakkwato da Kaduna.

Legit.ng ta tattaro cewa an kashe Mai garin Tunga tare da wasu mutum biyu a karamar hukumar Illela ta jihar Sakkwato a lokacin da wasu mahara suka afkawa kauyen yayin da ake sallar Magaruba a ranar Laraba, 24 ga watan Maris.

A cewar rahoton, maharan sun yi aiki na tsawan sa’a guda.

Yan bindiga sun kashe mutum 12 a sabbin hare-hare da suka kai garuruwan Kaduna da Sokoto
Yan bindiga sun kashe mutum 12 a sabbin hare-hare da suka kai garuruwan Kaduna da Sokoto Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Aliko Dangote da wasu yan Najeriya 2 sun shiga jerin mutum 7 da suka fi kowa kudi a Afirka

An samu labarin cewa an kaiwa kauyen Nasarawa a karamar hukumar Sabon Birni hari a rana guda amma ba a rasa rai ba.

Wani idon shaida, Ibrahim Adamu, ya ce maharani sun zo da kafa da misalin karfe 10:30 na dare.

“Sun shiga gidajenmu tare da karbe kudadenmu da kayan amfani. Sun zane matan da mazajensu suka gudu a yayin harin.”

Rahoton ya kuma bayyana cewa an kashe wasu mutum tara a hare-haren mabanbanta da aka kai a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a Jihar Kaduna.

Wani rahoton tsaro ya bayyana cewa ’yan bindigar sun shiga yankin Dogon Dawa zuwa Kuyello da ke kauyen a Birnin Gwari, inda suka harbe mutane shida.

An tattaro cewa wadanda suka rasa rayukansu sun hada da; Nura Rufai, Sanusi Gajere, Yakubu Labbo, Usman Dangiwa, Alhaji Abdulhamid da Janaidu Tsalhatu.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, ya ce an kuma kashe mutum biyu a Ungwan Maje.

KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Hanyoyin da za ka bi don yin rijistar jarabawar UTME na 2021

Ya kara da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya karbi rahoton faruwar lamarin cikin fushi da bacin rai, tare da addu’a ga wanda suka rasu da iyayensu.

A wani labarin, Shahararren malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya yi magana game da wasu daliban makarantun gandu ta Kaduna da aka yi garkuwa da su.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce umarnin da aka ba jami’an tsaro na harbe duk wanda su ka gani ya na dauke da bindigar AK-47 ya sa aka gaza ceto daliban.

Da yake magana da Daily Trust, malamin ya ce ya hadu da wasu ‘yan bindiga da su ka taimaka masa har ya gano gungun wadanda su ka sace wadannan dalibai.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng