Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria

Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria

- Rahoto ya nuna cewa an fitar da manyan motoci dari cike da albasa zuwa kasashen waje

- An tattaro cewa hakan na daga cikin matakin da dillalan albasa suka dauka na kauracewa kai kaya yankin kudu bayan rikicin Shasha da yayi sanadiyar mutuwar mambobinsu 27

- Sai dai kuma Shugaban masu noma albasa da siyar da ita, Aliyu Isa, ya musanta zargin cewa sun fitar da albasan ne saboda rikicin

Motoci dari daya dauke da albasa tan 4,000 sun bar Sakkwato zuwa wasu kasashen Afirka sakamakon rikicin kwanan nan day a afku a kasuwar Shasa da ke Ibadan, Jihar Oyo.

Rahotanni sun kawo cewa rikicin Shasa ya yi sanadiyyar mutuwar dillalan albasa 27 yayin da aka kona manyan motoci 14 kurmus.

Sai dai, Shugaban masu noma albasa da siyar da ita, Aliyu Isa, ya musanta cewa an yanke shawarar fitar da amfanin gonar ne sakamakon rikicin Shasa na kwanan nan.

Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria
Ta tabbata: Ba sauran kaiwa kudu kayan abinci, tirelolin Albasa sun bar Nigeria Hoto: Patrika
Asali: UGC

Daily Trust ta jiyo cewa wannan shi ne karon farko da aka gabatar da rahoton fitar da albasa a cikin kasar.

KU KARANTA KUMA: 2023: Jerin tsoffin gwamnoni shida da ke hararar kujerar shugabancin APC

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da shirin, wanda ya gudana a iyakar Illela, Isa ya lura cewa duniya na fuskantar matsalar albasa a duniya saboda masu matsaloli da kalubalen da annobar COVID-19 ta kawo.

Ya kara da cewa a Najeriya lamarin ya kara dagulewa ne sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a shekarar 2020, wanda hakan ya sanya ba a samu biyan bukatun albasa na shekara-shekara ba.

A cewarsa, Najeriya na samar da albasa mai nauyin metrik tan miliyan 1.4 a kowace shekara kuma tana fitar da albarkatun zuwa dukkan kasashen Afirka, ban da Masar da Jamhuriyar Nijar.

Ya ce kafin yanzu, basa kashe kasa da naira miliyan daya don fitar da amfanin gonarsu ta hanyar da ba ta dace ba, amma yanzu da suka yi rijista a hukumance; zasu kashe N100,000 kawai.

A nasa jawabin, kwanturolan Kwastam mai kula da jihohin Sakkwato da Zamfara, Alhaji Abdulhameed Ma’aji, ya ce sun samar da ingantattun mafita don saukaka fitar da kayyakin da ake samarwa a cikin Najeriya.

Shima da yake jawabi, Alhaji Ahmed Yahya, shugaban kwamitin bunkasa fitar da kayayyaki a Sakkwato, ya bayyana ci gaban a matsayin babban dagawa da kuma daukaka saboda kuwa ana ta fitar da kayayyaki ba bisa ka'ida ba a yankin.

KU KARANTA KUMA: Caccakar Buhari: DSS ta cafke hadimin Ganduje, Dawisu, bayan yace APC ta gaza

A wani labarin, Sunday Adeyemo, wani dan gwagwarmayar Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya fada wa gwamnatin tarayya da ta cire shi daga cikin jerin gwanon da take yi sannan ta bi shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da 'yan fashi.

Igboho ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a 26 ga Fabrairu, bayan da aka dakile kama shi da jami’an tsaro suka yi yunkurin yi.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun tsare motar dan fafutukan a hanyar babban titin Lagas-Ibadan.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel