Hotunan garejin kanikawa na mata zalla da aka bude a Sokoto
- Jelani Aliyu, shugaban NADDC ya kaddamar da bude sabon garejin mata zalla na gyaran ababen hawa
- An gano cewa wata kungiyar tallafawa mata me suna NANA ce ta kafa garejin inda ta horar da mata gyaran mota
- Aliyu ya jinjinawa wannan cigaba inda yace a manyan mujallu da gidajen talabijin na duniya kadai ake samu
Darakta janar na NADDC, Jelani Aliyu, ya kaddamar da sabon garejin gyaran ababen hawa na mata zalla a jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa garejin mai zaman kansa ne wanda NANA Girls and Women Empowerment Initiative suka kafa domin kafa tarihin gyaran ababen hawa ba ga maza ba kawai.
A yayin jawabi a taron, Aliyu ya taya sabbin kwararrun kanikawan mata murna inda ya bukaci su dage wurin aiki tukuru domin samun nasarori.
KU KARANTA: Ngwuta, alkalin kotun kolin Najeriya ya rasu a garin Abuja
Ya ce: "Ina alfahari da abinda ke faruwa yanzu haka. Wannan babban labari ne da muke karantawa ko kallo a manyan mujallu.
"Idan muka yi haka, ba mata da yara muke tallafawa ba, al'umma baki daya muke tallafawa.
“Ina matukar farin ciki da faruwar wannan lamari," ya kara da cewa.
Aliyu ya jinjinawa nagartar gidauniyar NANA da ta kafa garejin gyaran motan na mata na farko inda ya kwatanta shi da "cigaba mai kyau".
Kamar yadda yace, wannan cigaban ba ayyuka kadai zai samar ba, zai samar da mata injiniyoyi.
Darakta janar din ya kara da tabbatar da cewa zasu hada kai da NANA a wannan fannin domin basu tallafin da ya dace.
KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta magantu a kan gobarar da ta tashi a Aso Rock
A wani labari na daban, shugaban matasan jam'iyyar APC na gundumar Garki, Hon Babangida Sadiq Adamu a ranar Asabar da ta gabata ya aura mata biyu a rana daya a Abuja.
Adamu ya auri Malama Maimuna Mahmud da Malama Maryam Muhammad Na'ibi a ranar Asabar, 6 ga watan Maris din 2021.
Daurin auren farko an yi shi ne a masallacin Juma'a na Kada Bmiko kusa da makarantar firamare ta Kado Bmiko, 1st Avenue dake Gwarinpa da karfe 10:00 na safe.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng