Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki

Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki

- Gwamnan jihar Sakkwato ya zama na farko da ya yi gwajin mota mai aiki da lantarki a Najeriya

- An gabatar da motar ne a wani taron baje kolin kasuwanci da ke gudana jihar ta Sakkwato a makon nan

- Gwamna ya yabawa jagoran aikin kera motar, tare da jawo hankalin gwamnatin tarayya zuwa ga aikin

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya amshi motar Kona mai aiki da Wutar Lantarki wacce Hukumar Kula da kera motoci da cigaban motoci ta kasa (NADDC) tare da hadin gwiwar kamfanin Stallion suka bude kwanan nan.

Ku tuna cewa a ranar 5 ga watan Fabrairu, NADDC, a karkashin jagorancin Darakta-Janar na ta, Jelani Aliyu, ta gabatar da motar mai aiki da lantarki ta farko da aka kera a cikin gida mai suna Hyundai Kona, a Abuja.

Motar an sanya mata farashin Naira miliyan 24 ga kowane daya, tare da ba da garantin batir da kira na tsawon na shekara 5, 100% aiki da lantarki, ba amfani da mai za kuma a iya cajinta a gida da wajen aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gwamna ya Ganduje ya raka Bola Tinubu zuwa fadar Sarkin Kano

Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki
Ci gaba: Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Da yake jawabi bayan gwajin motar a gidan gwamnati na Sakkwato, Gwamna Tambuwal ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin wani sauyi na al'adu wanda zai shafi rayuwa da kuma damar 'yan Najeriya matuka.

A cewar Tambuwal, yana da kyau cewa yayin da nasarorin kimiyya a duniya ke turawa zuwa daina amfani da mai, Najeriya tana da nasarori irin na fasaha kamar mota mai aiki da lantarki da za ta kawo sauyi kan yadda ake ginin gidaje da kiyaye su, gina hanyoyi, da kuma sarrafa su.

Don haka gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan da suka dace wajen amfani da damar da Jihar Sakkwato ke da shi don tallafawa wajen fadada tattalin arzikin jihar.

Tambuwal, wanda ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da yake tuka mota mai amfani da lantarki, ya bayyana fasahar a matsayin mai ban sha’awa da kuma kyakkyawar muhalli, ya kara da cewa fasahar ta fi rahusa ta fuskar kulawa.

Gwamnan, yayin bayyana Mista Aliyu a matsayin babban jakadan jihar, ya ba da tabbacin goyon bayan sa ga NADDC a kokarinta na sauya fasalin kamfanin kera motoci na kasar.

Ya kuma yabawa babban daraktan NADDC bisa halartar kasuwar baje kolin, yana mai cewa kasancewarsa ya jawo zuba hannun jari da dama a jihar da yankin.

An gabatar da motar a wani baje kolin Kasuwanci na jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da ke gudana a Sakkwato, shugaban NADDC din dan shekara 55 ne ya gabatar da ita.

Shugaban na NADDC ya kasance tsohon ma'aikaci a America's General Motors wanda ake alfahari dashi don zanen wata mota a 2004 Pontiac G6 da 2010 Chevrolet Volt.

KU KARANTA: NDLEA ta kame wani tsoho dan shekara 70 dake kaiwa 'yan Boko Haram kwaya

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a 2019 Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin Buhari kan hanyoyin da za ta bi ta magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rahoto da Bloomberg ta fitar cewa Najeriya, itace kasa mafi yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya, da alama kuma za ta sake karya wani tarihin na zama kasa mai mafi yawan marasa aikin yi a duniya.

Atiku, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter kuma jaridar Legit ta gano ya bayyana cewa, gwamnatin mai ci a Najeriya na bukatar taimako don ceto kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.