Alkali ya sabunta laifukan da ake zargin dan hadimin Tambuwal da wasu mutum 2
- Wata kotun majistare a Sokoto ta kama dan hadimin Tambuwal tare da abokansa 2 da laifi dumu-dumu
- An kama su tun farko da laifin yada bidiyon tsiraicin wata budurwa wanda hakan yasa aka fasa aurenta
- Alkalin ya kama su dumu-dumu da wasu laifuka wanda daga bisani aka sabunta su bayan nazarin shari'ar
Wata kotun majistare da ke zama a Sokoto ta kama wasu matasa da laifin yada bidiyon tsiraicin wata yarinya a kafafen sada zumuntar zamani.
Wadanda ake zargin sune wani Aminu Tafida, da mai ada shawara na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Umar Abubakar da Mas'ud Gidado.
Amma kuma wanda ake zargi na hudu mai suna Aliyu Shehu kangiwa an wanke shi saboda bashi da wata alaka da wannan laifin, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Bidiyon jarumar yarinya tana fatattakar kattin 'yan fashi daga shagon mahaifiyarta da adda
Wadanda ake zargin tun farko an gurfanar da su a kan laifin rashin kamun kai, bata suna tare da cin zarafi wanda dan sanda mai gabatar da kara ASP Samuel Sule yace ya yi karantsaye ga sashi na 60, 377, 262, 48, 171, 173 da 379 na Penal Code ta jihar Sokoto.
Amma kuma alkali Shu'aibu Ahmad a hukuncinsa, ya ce bayan duba shari'ar a natse, ya sabunta laifukan da ake zarginsu da su.
KU KARANTA: Mai gidan haya ya lakadawa 'yar haya mugun duka, ta maka shi a gaban kotu
A wani labari na daban, Abduljabar Nasir Kabara, babban malamin da gwamnatin Kano ta haramtawa wa'azi ya maka gwamnatin jihar Kotu a kan tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba.
Gwamnatin Kano ta hana Kabara wa'azi a ranar 4 ga watan Fabrairun 2021 a kan zarginsa da wa'azi da zai iya tada zaune tsaye, The Cable ta wallafa.
A ranar 7 ga watan Fabrairu, gwamnatin jihar ta amince da mukabala tsakanin Sheikh Kabara da sauran malaman addini a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng