'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami

'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami

- 'Yan bindiga sun kai farmaki kauyensu ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi, kauyen Saketa dake Sokoto

- Dama kauyen yana karkashin karamar hukumar Bodinga ne dake jihar inda suka isa garin da tsakar dare

- Sun yi garkuwa da matar babban limamin garin da sirikarsa tare da kashe wani mutum daya sanan suka tsere

'Yan bindiga sun kai wa kauyensu ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi, dake karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto farmaki. A nan suka yi garkuwa da matar babban limamin kauyen.

An tattaro bayanai akan yadda 'yan bindiga suka addabi mazabar Dingyadi wacce take da kauyaku a kalla 18 a karkashinta.

An gano cewa 'yan bindigan sun isa kauyen ne a baburansu da daren Laraba ba tare da wasu jami'an tsaro sun dakatar dasu ba.

KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP na zargin APC da kitsa yadda za ta kwace jihar Zamfara

'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami
'Yan bindiga sun kutsa garinsu ministan 'yan sanda, sun sheke 1 tare da sace matar babban limami. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

Babban hadimin gwamna Aminu Tambuwal, Yusuf Dingyadi, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labari ta waya a ranar Alhamis.

A cewarsa: "Jiya da daddare, mun samu labarin cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyen Saketa dake Dingyadi dake karamar hukumar Bodinga hari. Sun kashe wani mutum sannan suka yi garkuwa da matar babban limamin garin da sirikarsa".

Dingyadi ya ce tuni kowa ya cigaba da harkokinsa a garin tun bayan an tura 'yan sanda don tabbatar da tsaro.

Har yanzu ba a samu damar tattaunawa da kakakin 'yan sandan yankin ba, Sanusi Abubakar, saboda an ji wayarsa a kashe take.

KU KARANTA: Abinda yasa ni da takwarana na jihar Bauchi muka ajiye takubbanmu, Ortom

A wani labari na daban, Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce ya shirya tsaf domin yin murabus idan hakan zai kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a wani shirin siyasarmu a yau wanda gidan talabijin na Channels TV ya shirya a ranar Laraba.

Ya ce: "Ban damu ba. Idan na san murabus dina a matsayin gwamna zai sa jama'a su kwanta bacci idanunsu biyu rufe, zan sauka daga mulkin."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel