Rikicin Makiyaya da Manoma: Mu Fulani ba 'yan ta'adda bane, in ji Sarkin Musulmi
- Sarkin musulmi ya bayyana cewa, Fulani ba 'ya ta'adda bane a matsayinsa na Bafulatani
- Sarkin ya jaddada cewa, akwai 'yan ta'adda a cikin Fulani amma ba kowa ne na banza ba
- Hakazalika ya nemi Fulani da musulmai kan su kasance masu bin doka da odar da gwamnati ta tsara
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce Fulani ba ‘yan ta’adda ba ne.
Ya fadi haka ne a Abuja jiya yayin ziyarar girmamawa ga ma'aikatan gudanarwa da sauran ma'aikatan Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Daily Trust ta ruwaito.
“Na riga na tsaya a kan wannan; mu ba 'yan ta'adda bane ba kuma masu aikata laifi ba. Tabbas, akwai 'yan ta'adda a tsakaninmu kuma hakan bai sanya dangi ko dukkan musulmai a matsayin masu aikata laifi ko yan ta'adda ba."
KU KARANTA: Masu bukulun na sayi jirage har 3 sai sun mutu a bakin ciki, Fasto Suleiman
“Ni Bafulatani ne mai alfahari da hakan kuma idan da zan mutu na sake dawowa zan roki Allah Ya dawo da ni a matsayin Bafulatani. Ni Bafulatani ne mai alfahari da zama Bafulatani amma ni ba mai aikata laifi bane, dan bindiga ko dan ta'adda ba," inji shi.
Sarkin ya bayyana kwarin gwiwar cewa aikin hajji na 2021 zai gudana tare da yin allurar rigakafin COVID-19, yana mai kira ga Musulmai da kada su sabawa dokar gwamnati kan kwayar cutar.
Ya yi nuni da cewa ana ci gaba da gudanar da tarurruka tsakanin malaman musulmai da gwamnati kan tabbacin allurar rigakafin don shawo kan musulmai kan lafiyar ta.
Tun da farko, Shugaban, NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan, ya ce hukumar tana tsara wata hanya da za ta ‘yantar da gwamnati daga nauyin kudi na hukumar ta hanyar hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce shirin ajiya na Hajji an yi shi ne don rage farashin ayyukan Hajji ga maniyyata da kuma ba wa matalauta daga cikin musulmai damar daukar nauyin kansu.
KU KARANTA: Su Burutai su godewa Allah ba lokacin da muke majalisa bane, in ji Shehu Sani
A wani labarin, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya roki Fulani makiyaya da kada su dauki bindiga AK-47 kuma su kasance cikin lumana.
Gwamnan, ya yi wannan rokon a jawabinsa a wajen kaddamar da allurar rigakafin dabbobi na shekara-shekara ta 2020/2021 da aka gudanar a Galambi Cattle Ranch dake Bauchi, ranar Laraba, ya bayyana Fulani a matsayin masu tawali’u, masu sauƙin kai, da kawaici.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng