APC zata shigar da ƙarar Hukumar zaɓe da PDP kan saka jam'iyyar cikin Zaɓe a Jihar Sokoto
-Jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta yi iƙirarain maka hukumar zaɓen jihar da kuma jam'iyyar PDP a kotu kan saka sunan jam'iyyar a takardar zaɓe.
- APC, ta bakin shugaban ta na jihar ta bayyana cewa hukumar zaɓen ta fito fili ta basu hakuri ko kuma su ɗau mataki tunda sun faɗa cewa baza su shiga zaɓen ba.
- An nemi jin ta bakin hukumar zaɓen amma ya ci tura saboda rashin amsa kiran wayar da sakataren hukumar ya yi
Jami'iyyar APC reshen jihar Sokoto ta yi barazanar cewa zata maka hukumar zaɓen jihar a kotu saboda saka tambarin jam'iyyar a cikin takardar zaɓen ƙananan hukumomi.
KARANTA ANAN: Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5
APC tace duk da tace ba zata yi takara a zaɓen ba amma hukumar zaɓen ta saka jam'iyyar a takardar zaɓen da aka yi ran Asabar, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.
A watan da ya gabata ne APC ta fitar da sanarwar cewa ba zata shiga zaɓen da gwamnatin jihar Sokoto ta shirya na ƙananan hukumomi da kansiloli ba.
APC tace hukumar zaɓen jihar yan koran PDP ne, don a cewarta 'ya'yan PDP ne kawai ɗauke da takardun zaɓen.
Lokacin da yake jawabi jim kaɗan bayan zaɓen, shugaban jam'iyyar APC na jihar, Isa Sadiq Achida, yace ya yi mamaki matuƙa da yaga tambarin jam'iyyar a cikin takardar zaɓe duk da matsayar ƙaurace ma zaɓen da jam'iyyar ta yi.
A cewar shugaban:
"Mun bayyana hukuncin da muka yanke kowa ya sani kuma bamu cike wata takarda da zata nuna muna son shiga zaɓen ba."
KARANTA ANAN: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno
"Amma mun yi matuƙar mamaki da muka ga an saka jam'iyyar mu a cikin takardun zaɓen harma wasu masu zaɓen sun kaɗa mana kuri'un su."
Ya ce hakan ta faru ne saboda jam'iyya mai mulkin jihar PDP na son cinma wani kuɗirin ta a jihar shiyasa aka sa APC a takardar zaɓen.
Shugaban ya kira yi hukumar zaɓen jihar "ta ba APC hakuri ko su makata ƙara a kotu kamar yadda doka ta tanadar."
An nemi sakataren hukumar zaɓen jihar ta wayar salula amma bai ɗaga ba haka kuma bai dawo da saƙon da aka tura masa ba.
A wani labarin kuma Sabon shugaban hukumar EFCC, Bawa ya fadi abu 1 da zai iya sa ya ajiye aiki
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya yi magana game da abin da zai sa shi ya bar kujerar da yake.
Abdulrasheed Bawa ya sha alwashin yin murabus daga shugaban EFCC idan aka bukaci ya yi abin da ya saba doka.
Asali: Legit.ng