'Yan bindiga sun harbe hadimin Sanata Aliyu Wammako a Sokoto

'Yan bindiga sun harbe hadimin Sanata Aliyu Wammako a Sokoto

- 'Yan bindiga sun hallaka wani mai taimakawa Sanata Ali Wammako da aka sace a jihar Sokoto

- An yi jana'izar marigayin a jihar Sokoto a daren jiya Juma'a a masallacin Sheikh Usman dan Fodiyo

- Jana'izar ta samu halartar jiga-jigai daga jam'iyyar APC, sarakunan gargajiya da Malamai

An harbe mai taimakawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Alhaji Abba Abbey Gidan Haki, wanda ’yan bindiga suka sace a daren Alhamis a Sokoto. Anyi jana'izar shi a daren Juma'a, The Nation ta ruwaito.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Usman dan Fodiyo dake Sokoto, Sheikh Abubakar Shehu Na Liman ne ya jagoranci sallar jana’izar.

Sallar jana’izar ta samu halartar Sanata Wamakko, Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi da shugaban riko na APC na jihar Sokoto,Alhaji Isa Sadiq Achida.

KU KARANTA: Shugaban kasar Amurka ya ci tuntube sau uku ya fado yayin hawa jirgin sama

'Yan bindiga sun harbe hadimin Sanata Aliyu Wammako a Sokoto
'Yan bindiga sun harbe hadimin Sanata Aliyu Wammako a Sokoto Hoto: dateline.ng
Source: UGC

Hakazalika da sarakunan gargajiya, Malaman Addinin Musulunci, mambobin Majalisar Kasa da ta Jiha, masu yi wa kasa hidima da wadanda suka yi ritaya da kuma dubunnan masu nuna juyayi, da sauran jama'ar gari.

Marigayin, a cewar wata sanarwa daga Bashir Rabe Mani, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Sanata Wamakko, tace ya rasu yana da shekaru 50.

Sanarwar ta ce, an sace Abbey ne aka kuma kashe shi duk a daren ranar Alhamis yayin da aka tsinci gawarsa a kan hanyar zuwa garin Durbawa da ke karamar Hukumar Kware ta Jihar Sakoto.

Ya bar mata daya da yara biyar.

Sanarwar ta roki Allah Madaukakin Sarki da Ya Rahamceshi ya ba shi gidan Aljannar Firdausi ya kuma ba iyalen sa, Wamakko da mutanen jihar babban kwarin gwiwar jure rashin.

KU KARANTA: NDLEA: Marwa yayi kira ga fara yiwa 'yan siyasa da dalibai gwajin shan kwayoyi

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce mutanenta sun kashe wasu 'yan bindiga biyu a Saminaka na karamar hukumar Lere ta jihar.

Rundunar ta kuma bayyana cewa abubuwan da aka kwato daga samamen sun hada da; bindigogin AK47 guda biyar, bindiga kirar G3 guda daya, tarin gidan alburusai guda 17 da kuma mota kirar Golf.

Kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, yana mai cewa, wasu ‘yan bindiga da yawa sun tsere zuwa cikin daji sun bar makaman su na aikata barna.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel