'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto

'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto

- Miyagun 'yan bindiga sun kaiwa fasinjojin dake kan hanyar zuwa Maulidin kasa a Sokoto hari

- An gano cewa 'yan bindigan sun kwashe fasinjoji masu yawa a hanyar Kankara zuwa Sheme

- Duk da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ya musanta, mazauna yankin sun tabbatar

Fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami'an 'yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta wanke matar da ake zargi da sheke mijinta ta hanyar yi wa mijinta allurar guba

'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto
'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Majiyoyin sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne wurin karfe 11 na daren Alhamis da jama'ar ke tafiya a manyan motoci kirar bas.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya musanta aukuwar lamarin inda yace babu fasinjan da aka sace amma sun yi gaba da gaba da 'yan bindiga sai suka tsere cikin dajika.

SP Isah yace an ga dukkan fasinjojin da suka tsere zuwa dajikan kuma sun kai 43 cif.

"Ba gaskiya bane. Abinda ya faru a daren Alhamis shine, an samu wasu fasinjoji daga jihar Gombe a kan hanyarsu ta zuwa Maulidi a Sokoto.

"A tsakanin Sheme da Kankara, ina tunanin 'yan bindiga sun bullo musu amma sai suka bar ababen hawansu suka shiga daji domin tsira.

"Da safen nan jami'anmu tare da DPO suka shiga daji nemansu kuma duk an gansu a halin yanzu," Isah yace.

KU KARANTA: Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi

A wani labari na daban, a ranar Juma'a ne jihar Kaduna ta tashi da mummunan labarin sace dalibai mata a kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Mando a jihar Kaduna.

Makarantar na da nisan kasa da kilomita 15 daga makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna (NDA).

A ranar Alhamis ne 'yan bindiga suka kai hari kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun inda suka halaka mutane bakwai. An gano cewa 'yan bindiga sun raunata wasu tare da sace shanu 20.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel