Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal

Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal

- Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana cewa ta kashe makudan kudade don dauke nauyin dalibai

- Kimanin N740m aka kashe domin yiwa dalibai rajistar WAEC da NECO a fadin jihar

- Hakazalika gwamnatin jihar ta shirya kirkirar wani shiri don karfafa matasa a fadin jihar

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kashe Naira miliyan 740 don biyan kudin rajistar Hukumar Kula da Jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da Majalisar Rajistar Jarabawa ta Kasa (NECO) don daliban jihar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin rantsar da zababbun shuwagabannin kungiyar Matasan Najeriya (NYCN) da kuma Kungiyar Daliban Makarantar Sakkwato (FOSSOSA).

An gudanar taron ne a dakin taro na cibiyar koyar da karatun Alkur’ani ta Sultan Maccido dake Sakkwato, This Day ta ruwaito.

KU KARANTA: Rashin aikin yi ne ya tilasta ni yin fashi, in ji wani matashi mai skekaru 23

Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal
Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal Hoto: The Sun Nigeria
Asali: UGC

A wata sanarwa daga mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Muhammad Bello, Tambuwal ya ce a yanzu haka gwamnatin jihar na ci gaba da shirye-shiryen gabatar da shirin tallafawa matasa na bunkasa tattalin arzikin Sakkwato (SO-YEEP).

A cewar gwamnan, an tsara shirin ne domin ya kunshi dubban matasa a dukkanin runfunan zabe 3,032 na kananan hukumomi 23 na jihar.

Tambuwal ya ci gaba da bayanin cewa aikin zai hada da koyar da sana’o’i, bayar da kudi kai tsaye da kuma jagoranci.

"Wannan ci gaba ne da kokarin da muke yi na sanya matasan Sakkwato ba wai kawai dogaro da kai ba har ma da daukar ma'aikata da kirkirar arziki," ya kara da cewa, yayin kalubalantar su da su mai da hankali sosai ga cimma burin ci gaban matasa na gwamnatinsa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta dawo da 'yan gudun hijirar Borno 4,982 daga Kamaru

A wani labarin, A cewar wasu masu yada ilimin Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), idan aka zo batun shiga STEM, alkaluman suna kan raguwa a Arewacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Masu ba da shawara na STEM sun ce wannan raguwar za a iya danganta shi da dalilai da yawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.