Jihar Sokoto
Kungiyar Fulani makiyaya ta (MACBAN) ta bukaci a kare martaba da kimar kujerar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III. Ta gargadi gwamnatin Sokoto.
Rundunar sojin Najeriya ta fafata da yan bindiga a jihar sokoto inda ta kashe guda biyar tare da kwato mutane biyu da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Gudu.
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa hakiman da suka shigar da kara bayan tsige su sun makara. Kwamishinan shari'a na jihar ne, Barista Nasiru Binji ya fadi haka.
Shugaban kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bukaci a soke dokar da ta ba gwamnatin jihar Sokoto damar sauke Sarkin Musulmi daga kujera.
Yayin da rikicin masarauta ke kara kamari a Sokoto, babbar kotun jiha ta dakatar da gwamna Ahmed Aliyu daga tsige hakimai biyu da ta dakatar a baya.
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya gargadi jami'an sojoji da su kaucewa duk wani lamari da ya shafi kabilanci ko bangarancin addini inda hakan zai raba Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi martani bayan kisan Farfesa Yusuf da Birgediya Janar Harold a Abuja. Ya fadi mafita kan matsalar yan bindiga.
Kungiyar addinin Musulunci MURIC mai gwagwarmayar kare hakƙin al'ummar Musulmin Najeriya ta nanata cewa har yanzun kujerar Sarkin Musulmi na tsaka mai wuya.
Kudurin sabunta dokar Masarautar Sokoto ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren majalisar Sokoto. Ana fargabar kudurinzai rage ikon Sarkin Musulmi
Jihar Sokoto
Samu kari