Wata Cuta Mai Saurin Yaduwa Ta Barke a Sokoto, Ta Hallaka Mutum 23 Wasu 260 Sun Kamu
- Wata cuta dake jawo kumburin ciki da ƴaƴan hanji ta ɓarke a wasu kauyukan jihar Sokoto
- Kwamishinan lafiya na jihar, Muhammed Iname, yace cutar ta hallaka aƙalla mutum 23 wasu 260 sun kamu
- Iname ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da duk abinda ya kamata domin dakile yaɗuwar cutar
Sokoto:- Akalla mutum 23 sun mutu sanadiyyar barkewar wata cuta da ake kira 'gastroenteritis' amma an fi sanin ta da murar ciki a wasu ƙauyukan Sokoto.
Kwamishinan lafiya na jihar, Muhammed Iname, shine ya tabbatar da haka a taron manema labarai ranar Talata.
Ya bayyana cewa ɓarkewar cutar ya shafi kananan hukumomi 13 cikin 23 da ake da su a jihar Sokoto, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Kwamishinan ya ƙara da cewa sama da mutum 260 sun harbu da cutar ta murar ciki zuwa yanzun, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Kananan hukumomin da abun ya shafa sun haɗa da Dange/Shuni, Kebne, Gwadabawa, Tangaza, Isa, Bodinga, Wamakko, da kuma Silame.
Menene alamun kamuwa da cutar?
Ana gane mutum ya kamu da cutar ne idan aka ga waɗannan alamun a tattare da shi, sun haɗa da, Amai, Zawo, zazzabi da tashin zuciya.
Kuma mutane na kamuwa da cutar ne idan suka yi mu'amala da mai ɗauke da ita ko suka yi amfani da abinci ko ruwa da mai cutar yayi amfani da shi.
Hukumomi a Sokoto sun bayyana cewa cutar tafi muni a ƙaramar hukumar Gwadabawa inda mutum 47 suka harbu.
Wane mataki gwamnati ta ɗauka?
Kwamishinan ya bukaci yan jihar da su kula sosai domin cutar tana da saurin yaɗuwa daga wannan zuwa wancan.
Muhammed Iname yace:
"Ya kamata mutane su kula sosai, su rage yawan zuwa yankunan da cutar ta shafa domin an gano cewa tana da saurin yaɗuwa a tsakanin mutane."
"Muna gargaɗin ma'aikatan lafiya su daina duba masu ɗauke da cutar a gida domin gwamnati ta samar da duk abinda ya kamata wajen dakile cutar."
Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama
Iname ya shawarci mazauna jihar da su cigaba da gudanar da ayyuakansu na yau da kullum yayin da gwamnati take sanya ido kan lamarin.
A wani labarin kuma Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan
Yayin da ake zargin jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu na jinya ne a birnin Landan, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wasu magoya bayansa sun bayyana hotunansa tare da gwamnan Lagos, Babajide Sanwo Olu.
Asali: Legit.ng