Sarkin Musulmi ya bayyana 'yan Boko a matsayin matsalar Najeriya
- Sarkin musulmi ya bayyana cewa, 'yan boko su ne matsalar Najeriya a halin da ake ciki
- Ya bayyana haka ne a jihar Gombe yayin wani taron da ya gudana na addinai a jihar ta Gombe
- Ya kuma kalubalanci shugabanni da cewa su koma ga littafan addininsu domin samun mafita
Gombe - Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ’yan boko da masu fada aji a kasar nan sune matsalar Najeriya.
Alhaji Sa’ad Abubakar ya fadi hakan ne a yayin wani taron wanzar da zaman lafiya da gina kasa da Kwamitin Shirya Da’awah na Kasa ya shirya karo na uku a Jihar Gombe.
Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, a yayin taron ne kwamitin wanda ya hada mabiya addinin Kirista da Musulmi ya tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya a kasar nan.
A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabannin da cewa su koma wa littatafan su masu tsarki don samun ginshikin shugabanci na gari.
A cewarsa, muddin aka rasa kyakkyawan shugabanci to za a rasa zaman lafiya da hakan zai tarwatsa duk wani hadin kai a tsakanin al’umma.
A farko tun kafin taron ne Sarkin Musulmin ya jagoranci bude wata hanya a garin Gombe da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gina kuma aka sanya mata sunansa a Unguwar Gandu da ke bayan gidan Sarkin Gombe.
Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7
A ranar Talata ne Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kan wasu al’ummu bakwai da ke karamar hukumar Balanga ta jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ismaila Uba-Misilli, Darakta-Janar na harkokin yada labarai, na gidan gwamnatin Gombe ya fitar.
Mista Uba-Misilli ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Njodi ne ya bayyana hakan.
An ruwaito Mista Njodi yana cewa matakin ya biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja a cikin al'ummomin a safiyar Talata 27 ga watan Yuli, VON ta ruwaito.
Sojoji sun garkame kasuwannin jihar kudu saboda nuna goyo baya ga Nnamdi Kanu
A wani labarin, Jihar Imo - Sojoji a ranar Talata sun hana ‘yan kasuwa a kasuwannin katako da na kayayyakin gini a Orlu, jihar Imo, budewa domin gudanar da kasuwancinsu na ranar.
Mafi yawan ‘yan kasuwar a kasuwannin biyu a ranar Litinin din da ta gabata sun ki bude shagunansu don nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar tuhumar ta’addanci a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Sojojin, wadanda ke gudanar da aikin shingen binciken ababen hawa kusa da manyan kasuwannin biyu a Orlu, sun hana ‘yan kasuwar bude shagunansu da duk wata harkar kasuwanci.
Asali: Legit.ng