Kotun Sokoto ta yanke wa dalibin jami’a shekaru 10 a gidan yari
- Babbar Kotun Jihar Sokoto ta kammala sauraren karar da ta shigar kan wani dalibin jami’ar jihar Sokoto, Joseph Oladapo Philips
- Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta zargi dalibin da keta wasu sassan dokar Penal Code ta Jihar Sokoto
- Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar ta bayyana yadda wanda ake karar ya samu kudade ta hanyar rashin gaskiya daga wadanda abin ya cika da su
wata kotun jihar Sokoto ta yanke wa wani dalibin jami’ar jihar Sokoto, Joseph Oladapo Philips, hukuncin daurin shekaru 10 kan damfara ta yanar gizo.
An yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, 2021, bayan da ofishin Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) shiyyar Sakkwato ta gurfanar da dalibin a kotu, hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa ta Facebook.
Hukuncin
Alkalin kotun, Mai shari’a Mohammed Sifawa, ya samu wanda ake tuhumar da laifin karbar sama da Naira miliyan 7 ($ 18,700) daga hannun wadanda abin ya shafa da sunan wani sojan Amurka da ke aiki a Afghanistan.
Laifin daya da aka tuhume shi da shi ya kasance kamar haka:
"Cewa kai Joseph Oladapo Philips "namiji" a wani lokaci a 2021 a Sakkwato a tsakanin sashin shari'a na Babbar Kotun Jihar Sakkwato, ka damfari wata Lisa Farley daga North Carolina da Joey Jaitrong ta hanyar yaudararsu da rashin gaskiya ta hanyar karbar kudi $ 18,700 ka gabatar da kanka gare su a matsayin sojan Amurka da aka tura Afghanistan sannan ka tura musu takardun bogi ta hanyar shafin ka na Instagram wanda ka san karya ne kuma hakan ka aikata laifi wanda ya sabawa Sashe na 310 na Dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Sakkwato kuma hukuncinsa na a karkashin Sashe na 311 na wannan Doka.''
Philips ya amsa laifinsa kuma kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 tare da zabin N500,000.
An kuma umarci mai laifin da ya biya dalar Amurka $ 18,700 a matsayin diyya ga wanda ya damfara ta hannun EFCC.
EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina
A wani labarin kuma, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Kano ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta hanyar intanet a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.
Hukumar, a cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook, ta ce wadanda ake zargin galibinsu matasa ne da shekarunsu basu wuce 20 ba.
Sakamakon binciken da jaridar The Nation ta gudanar ya nuna cewa galibin daliban jami’a ne da matasa marasa aikin yi.
Asali: Legit.ng