Nasara daga Allah: Danmaraki, Sama'ilo da wasu shugabannin 'yan bindiga sama da 20 na neman rangwame

Nasara daga Allah: Danmaraki, Sama'ilo da wasu shugabannin 'yan bindiga sama da 20 na neman rangwame

  • Sakamakon bamabaman da sojoji suke harbawa dajika, ‘yan bindiga sun fara laushi don yanzu haka sun fara neman gafarar hukuma
  • Manyan shugabannin ‘yan ta’addan da suke arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar kasar nan sun fara zubar da makamansu
  • Kamar yadda majiya mai karfi ta tabbatar, sun fara lallabawa a asirce wurin sojoji don bayyana tubarsu don su samu sassauci

Sakamakon ruwan bama-baman da ‘yan bindiga suke jefawa dajikan da suke jihohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiyan kasar nan, 'yan bindiga sun fara laushi suna zubar da makamansu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta bayyana yadda wasu manyan takadaran ‘yan bindiga suka fara mika wuya suna zubar da makamansu.

KU KARANTA: El-Rufai ya sanar da abinda suke yi da gwamnatin Nasarawa wurin ceto basaraken jiharsa

Jami'in tsaro yayi bayani

Kamar yadda jami’in ya tabbatar:

Wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindiga fiye da 20 da sauran shugabannin ‘yan ta’addan sun fara lallabawa cikin sirri suna rokon jami’an tsaro yafiya da kuma sassauci.

Kara karanta wannan

Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

Sun dade suna addabar kauyuka da mazauna yankunan Zamfara, Neja, Kaduna da sauran jihohi na arewa maso yamma da arewa ta tsakiya tsawon shekaru.
Ina mai tabbatar muku da cewa daga Samaila Danmaraki da sauran miyagun shu’uman ‘yan bindiga sun fara ji a jikinsu suna rokon gafara da sauki a hannun sojojin Najeriya. Yanzu haka suna so gwamnati ta yafe musu,” a cewarsa.

Gwamnati bata riga ta aminta da tuban 'yan bindigan ba

Saidai sojan da ya sanar da hakan yaki bayar da sunansa a cewarsa shugabanni sun ki amincewa da ‘yan bindiga.

A cewarsa har yanzu suna auna neman yafiyar ‘yan bindiga da kuma sanin asalin gaskiyar kudirinsu saboda sanin gaskiyar halinsu na ta’addanci, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yanzu mun yi shiru ne muna sauraron wannan yarjejeniyar dake tsakanin shugabannin siyasa da shugabannin addinai na islama da kirista don tattaunawa akan illar da hakan zai haifar. Muna tsoron kada mutane da dama su cutu sakamakon yafe wa ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gidan ya cabe, bangaren Lai Mohammed sun sa sharadin barin APC

KU KARANTA: Matawalle ya bayyana abinda ke assasa ta'addanci a Zamfara

Miyagu sun sheke dan takarar shugabancin karamar hukuma a Kaduna

Dan takarar jam'iyyar All Progressive Chairmanship Congress (APC) na karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, Alamkah Dominic Usman wanda aka fi sani Cashman ya sheka lahira bayan wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe shi a jihar Benue.

A yayin zantawa da Daily Trust, shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Kachia, Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, ya ce an harbe Usman a wani wuri a jihar Benue.

Alhaji Sulaiman ya ce, Usman amintaccen dan jam'iyya ne kuma ya hadu da ajalinsa ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Binuwai inda iyalinsa ke zama, bai san cewa yana dab da amsa kiran ubangijinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel