Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko ya aurar da 'ya'ya 10 a gidansa dake Gawon Nama a jihar Sokoto
  • Wannan gagarumin biki kuwa ya samu bakuncin ministan harkokin 'yan sanda, ministan shari'a da sauran manyan 'yan siyasa
  • Fitaccen mai arzikin dan kasuwa na jihar Katsina, Alhjai Dahiru Mangal ya samu damar halartar gagarumin bikin

Sokoto - Ministan kula da harkokin 'yan sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, Ministan shari'a, Abubakar Malami da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, suna daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin auren 'ya'ya 10 na Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a ranar Lahadi.

Daily Trust ta tattaro cewa ministocin sun wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a wurin bikin.

Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko
Malami, Dingyadi, da sauran jiga-jigan da suka halarci auren 'ya'ya 10 na Wamakko. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Facebook

Sauran jiga-jigan da suka halarci bikin sun hada da tsoffin Gwamnonin Sokoto da Zamfara, Yahaya Abdulkareem da Abdulazeez Yari, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahya Abdullahi wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawal da sauran 'yan majalisu.

Kara karanta wannan

Hotunan shagalin 'Luncheon' na auren Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Bayero

Fittaccen attajirin mai kudi kuma dan kasuwa na jihar Katsina, Dahiru Mangal, ya halarci bikin auren a gidan tsohon gwamnan dake Gawon Nama a jihar Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An daura auren a ranar Lahadi yayin da ake liyafar cin abincin rana ta bikin dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Kano, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Nasir Bayero.

Liyafar cin abincin ranan ta karba manyan mutane da fitattun 'yan siyasa da suka je taya shugaban kasan murnar aurar da dan shi.

Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF

A wani labari na daban, Manjo janar Abdul-Khalifah Ibrahim, kwamandan sojojin MNJTF ya bukaci rundunonin soji da su shirya ragargazar ragowar mayakan Boko Haram da suke wuraren tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Hotunan Aisha Buhari lokacin da take jiran isowar amaryar dan ta Yusuf Buhari

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Juma’a, Shugaban fannin yada labaran soji na MNJTF, Kanal Muhammad Dole ya ce Ibrahim yayi wannan maganar ne a lokacin da ya zagaya sansanonin sojojin yankin.

Dole ya ce a makon da ya gabata kwamandan ya kai ziyara bangare na uku dake Monguno a Najeriya, bangare na daya dake Moura a Kamaru da bangare na boyu dake Bagasola a Chadi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel