Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto
- Wasu yan bindiga sun hallaka mutane tare da jikkata wasu a kauyuka uku dake jihar Sokoto
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun mamayi Benjigo, Dantudu da Tulutu dake karamar hukumar Goronyo ranar Asabar
- Jihar Sokoto dake cikin yankin arewa maso gabas na fama da harin yan bindiga da kuma satar mutane domin neman kuɗin fansa
Sokoto - Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 9 tare da sace wasu shida a wani hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Channels tv ta ruwaito cewa harin ya shafi ƙauyuka uku da suka hada da, Bejingo, Dantudu da kuma Tulutu.
Wata majiya daga yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa maharan sun kashe maza 8 tare da wata mace ɗaya ranar Asabar.
Yace: "Maharan sun kashe maza 8 da kuma wata mace ɗaya, yayin da suka jikkata wasu da dama."
Maharan sun yi awon gaba da dabbobi
Hakazalika rahoto ya nuna cewa yan bindiga sun yi awon gaba da dabbobi masu yawa waɗanda ba'a san iyakar adadin su ba.
Mutanen dake zaune a kauyukan sun fara ficewa zuwa makotansu domin tseratar da rayuwarsu daga yan bindigan.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka
Har yanzun hukumar yan sanda bata ce komai ba game da lamarin domin kakakin hukumar ta jihar, Muhammad Sadiq, yace babu wani rahoto da suka samu kan harin.
An yiwa gawarwakin waɗanda aka kashe jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya koyar.
Sokoto, na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso yammacin ƙasar nan da matsalar taro ta shafa, inda take fuskantar harin yan bindiga da kuma satar mutane domin neman kuɗin fansa.
A watan da ya gabata, yan bindiga sun kashe mutum 2 tare da sace matafiya sama da 60 a kan babbar hanyar Sokoto-Gusau.
A wani labarin kuma Sojoji Sun Ceto Karin Mutum 7 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos
Sojojin Najeriya a jihar Filato na Opertaion Safe Haven sun bayyana cewa sun ceto ƙarin mutum 7 daga cikin waɗanda harin Jos ya rutsa da su.
Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kaiwa matafiya a kan hanyar Rukuba, karamar hukumar Jos ta arewa , jihar Filato.
Asali: Legit.ng