Matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau ba 60 ba – ‘Yan sanda

Matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau ba 60 ba – ‘Yan sanda

  • Hukumar 'Yan sandan jihar Zamfara ta ce matafiya tara kawai aka sace a hanyar Sokoto zuwa Gusau sabanin 60 da ake ta yayatawa
  • Kakakin rundunar ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 27 ga watan Yuli
  • Ya kuma bayyana cewa jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu don ganin sun kubutar da wadanda lamarin ya ritsa da su

Gusau, Jihar Zamfara- Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, ta bayyana cewa matafiya tara aka sace a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau a ranar Lahadi, sabanin 60 da ake ta yayatawa.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a Zamfara, Muhammad Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ga manema labarai, jaridun Premium Times da The Cable suka ruwaito.

Matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau ba 60 ba – ‘Yan sanda
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce:

“A ranar Lahadi 25 ga watan Yuli, 2021, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun tare wata Mota kirar Toyota mallakar hukumar jihar Sakkwato tare da sace fasinjoji goma sha daya (11) wadanda ke tafiya daga Sakkwato zuwa Abuja a hanyar Sakkwato-Gusau a karamar Hukumar Bakura.

Kara karanta wannan

Kotun Sokoto ta yanke wa dalibin jami’a shekaru 10 a gidan yari

“An sanar da jami’an‘ yan sanda da ke aiki don dawo da zaman lafiya, kuma cikin hanzari suka bazama zuwa wurin suka fatattaki ‘yan bindigar wadanda suka tare motoci da yawa don yin garkuwa da su.
“Nan take aka kakkabe hanyar domin masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar sannan kuma aka tura karin jami’an 'yan sanda domin inganta tsaro da lafiyar matafiya.
“A lokacin da suke kan hanya, an ga wata Motar Toyota Bus wacce mallakar Jihar Sakkwato ce babu kowa a ciki kuma an bayyana cewa an sace fasinjoji 11 ciki har da direban, kuma an yi cikin daji da su kafin isowar 'yan sanda.
"Jami’an sun ci gaba da aikin bincike da kuma ceto a dajin da nufin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su. Yan daban sun yi watsi da mutum biyu da aka barsu a baya tare saboda tsoron kada yan sanda su kashe su, sun tafi da sauran mutum tara da abun ya cika da su cikin daji. Rundunar a yanzu haka tana amfani da dabaru daban-daban da nufin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

"Saboda la'akari da abin da ke sama, rundunar ta umarci jama'a da su yi watsi da batun sace mutane 60. A gefe guda kuma, ana kira ga ‘yan jarida da su tabbatar da ingancin duk wani bayani da zai zo musu kafin su je ga jama’a.”

'Yan Bindiga Sun Tare Babban Hanyan Sokoto Zuwa Gusau, Sun Sace Motocci 3 Maƙil Da Matafiya

A baya mun ji cewa 'Yan fashin daji a ranar Lahadi sun tare hanyar Sokoto zuwa Gusau sun sace fasinjoji da ke cikin motoccin bus guda uku mallakar hukumar sufuri ta jihar Sokoto, rahoton The Punch.

Wani mai mota, Alhaji Mohammed Yusuf, da ya tsallake rijiya da baya yayin harin, ya shaidawa The Punch cewa yan fashin sun tare hanyar ne kusa da Dogon Karfe misalin karfe 3 na rana suka sace dukkan fasinjojin da ke cikin motoccin uku.

Yusuf ya kara da cewa a yayin da yan bindigan suka shiga daji tare da wadanda suka sace, sauran masu motoccin, har da shi, sun wuce da sauri kada yan bindigan su dawo su sace su.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara a ranar idi

Asali: Legit.ng

Online view pixel