Yan Bindiga Sun Sheke Mutum 2 Tare da Awon Gaba da Wasu Mutane Kusan 100 a Sokoto

Yan Bindiga Sun Sheke Mutum 2 Tare da Awon Gaba da Wasu Mutane Kusan 100 a Sokoto

  • Wasu yan bindiga sun hallaka mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama a jihar Sokoto
  • Ɓarayin sun tare manyan hanyoyin Sokoto-Gusau da kuma Wurno-Goronyo duk a rana ɗaya
  • A halin yanzun jami'an yan sanda na kan bincike domin tabbatar da mutanen da lamarin ya shafa

Wasu yan bindiga sun toshe manyan hanyoyi biyu a jihar Sokoto, inda daga bisani suka kashe mutum biyu kuma suka yi awon gaba da wasu da dama ranar Lahadi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hanyoyin da yan bindigan suka tare sun haɗa da hanyar Sokoto-Gusau, inda akalla suka yi awon gaba da mutum 60 da safiyar Lahadi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Hakanan kuma sun tarbe hanyar Wurno-Goronyo da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar, inda suka kashe mutum biyu sannan suka sace wasu da yawa.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Yan bindiga sun kai hari sau biyu a jihar Sokoto
Yan Bindiga Sun Sheke Mutum 2 Tare da Awon Gaba da Wasu Mutane Kusan 100 a Sokoto Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shugaban wani kamfanin tafiye-tafiye na jihar, Yahuza Abubakar Chika, wanda ya tabbatar da harin hanyar Sokoto-Gusau, yace lamarin ya rutsa da motar bas ɗinsu ɗaya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Direban motar da fasinja ɗaya sun tsira ba tare da an cutar da su ba, amma sauran fasinjojin motar yan bindigan sun tafi da su cikin daji," inji shi.

Yan bindiga sun kashe mutum biyu

Hakanan kuma da yake tabbatar da harin kan hanyar Wurno-Goronyo, shugaban ƙaramar hukumar Wurno, Abubakar Arzika, yace an kashe mutum biyu cikinsu harda mace ɗaya.

Sai-dai Arzika ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da mutum nawa ne yan bindigan suka yi awon gaba da su ba, inda ya kara da cewa a halin yanzun jami'an yan sanda na kan bincike.

An nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, amma ba'a same shi ba.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

A wani labarin kuma Dakarun Soji Sun Damke Mutum 19 Dake Tallafawa Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Jami'an sojin ƙasa sun samu nasarar kama mutum 19 dake tallafawa yan bindiga a Zamfara.

An kama mutanen ne da laifin bada bayani domin a sace wani ko kuma suce a kashe wani a ƙauyen Ɗansadau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel