Da Duminsa: Tawagar Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin Sace Mace Mai Juna Biyu a Sokoto

Da Duminsa: Tawagar Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin Sace Mace Mai Juna Biyu a Sokoto

  • Wata tawagar yan bindiga sun gamu da fushin dakarun soji yayin da suka sace wata mata mai juna biyu a Sokoto
  • Sojojin sun harbe yan bindigan har lahira sannan suka taimakawa matar ta haifi jaririnta
  • Dakarun sojojin sun kwato makami da suka hada da bindigu, mashin, motoci da sauransu

Sokoto - Wasu yan bindiga da suka yi kokarin sace mace mai juna biyu an harbe su har lahira a jihar Sokoto, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar tsaro, Benard Onyeuko, shine ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar tsaro dake Abuja.

Yace dakarun rundunar sojin ƙasa na operation hadarin daji sun ragargaji yan bindiga 14 dake aikata ta'addanci a ƙauyen Eldabala, karamar hukumar Tangaza, jihar Sokoto.

Onyueko ya kara da cewa sojojin sun samu nasarar kuɓutar da mutane 35 daga hannun yan ta'addan.

Yan bindiga sun gamu da ajalinsu yayin sace mace mai ciki
Da Duminsa: Tawagar Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu Yayin da Suka Yi Kokarin Sace Mace Mai Juna Biyu Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Sojoji sun taimakawa matar ta haihu

Kara karanta wannan

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

Wani ɓangaren jawabinsa yace:

"Sojojin sun kwato bindigu kirar AK-47 guda bakwai, mashin guda shida, kayan sojoji da yan sanda, motoci 6 da dai sauran su."
"Hakanan kuma jami'an sojin sun taimakawa ɗaya daga cikin waɗanda ɓarayin suka yi kokarin sacewa ta haihu cikin koshin lafiya."

Ya kara da cewa gwarazan sojojin sun damke masu taimakawa yan bindigan da bayanai mutum 16, da wani mayaudari da ya bayyana kansa da Corporal.

Jawabin ya kara da cewa:

"Tsakanin 16 zuwa 29 ga watan Yuli, sojojin mu sun kai ɗaukei a kiran waya da aka musu kan harin yan bindiga da yan ta'adda a kauyukan Hanutaru da Ɗansadau dake karamar hukumar Maru."
"Aƙalla yan bindiga 14 ne suka kashe yayin da suka kuɓutar da mutane 36 da aka sace a cikin wannan lokacin."

A wani labarin kuma Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Kano

Gwamnatin jihar Kano, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa babu wani shiri na hana mata tukin mota a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba, shine ya faɗi haka yayin da yake martani kan jita-jitar dake yawo cewa gwamnatin jihar na shirye-shiryen kafa dokar hana mata tuki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel