'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal

'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal

  • Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto ya ce 'yan sa kai zasu jagoranci jami'an tsaro a yaki da 'yan bindiga
  • Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da sarakunan gargajiya na jihar suka ziyarcesa a gidan gwamnatin jihar
  • Gwamnan yace 'yan sa kan sun fi jami'an tsaro sanin dajika da sansanin 'yan bindigan dake barna a jiharsa

Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a jiya ya ce 'yan sa kai ne zasu jagoranci jami'an tsaro wurin yaki da miyagun 'yan bindiga a jihar.

Ya sanar da hakan ne yayin da sarakunan gargajiya na jihar suka kai gaisuwar sallah gidan gwamnatin jihar. Sarakunan sun samu jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar.

KU KARANTA: Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal
'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwamnan ya ce 'yan sa kan sun san dajin sosai kuma nan ne maboyar miyagun 'yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe

"Bamu da 'yan sa kai a Sokoto. Amma abinda muke kokarin yi shine hada wata tawagar 'yan sa kai tare da masarautar jihar wadanda zasu iya jagorantar jami'an tsaro cikin dajikan da suka yi wa 'yan bindiga sansani," yace.

Amma kuma, ya ce yaki da 'yan bindiga za a samu nasararsa ne da goyon baya tare da tallafin mazauna yankin.

Kamar yadda yace, akwai 'yan yanki dake taimakawa 'yan bindigan kuma ya zama dole a tsamo su.

"Wadannan mutanen suna kai farmaki yankunanmu cike da nasara saboda suna da masu kai musu bayanai daga cikinmu.

“Dole ne jama'armu su dauka mataki ta hanyar kawo rahotannin masu kaiwa 'yan bindiga da masu taimaka musu ga jami'an tsaro.

“Saboda sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin boyewa," yace.

Wasu daga cikin sarakunan gargajiyan sun nuna damuwarsu kan yadda kashe-kashe suka tsananta a yankunan, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A wani labari na daban, Manjo Janar Christopher Musa, kwamandan rundunar hadin guiwa ta tsaro dake yankin arewa maso gabas ta Operation HADIN KAI (OPHK) yayi kira ga sojojin sashin da su mamaye dukkan yankunan domin yakar ta'addanci tare da dawo da zaman lafiya.

Musa ya bada wannan umarnin ne yayin ziyarar da ya kaiwa dakarun bataliya ta 68 da birged ta 5 dake filin daga na Malam Fatori da Damasak.

Ya je duba yanayin ayyukan dakarun da kuma hanyar gane juna da gabatar da kanshi ga dakarun da aka tura yankin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel