Hoton Hatsabibin Ɗan Bindigan Sokoto Da Aka Kama a Gidan Karuwai Bayan Shafe Shekaru Ana Nemansa Ruwa a Jallo
- Jami'an NSCDC a jihar Sokoto sun kama wani dan bindiga Bello Galadima a gidan karuwai
- An kama Bello Galadima ne a unguwa Aliyu Jodi sakamakon bayyanan sirri da aka samu
- A halin yanzu Galadima yana can ana masa tambayoyi kuma yana bada bayanai masu amfani
Hukumar tsaro ta NSCDC ta kama wani hatsabibin dan bindiga, Bello Galadima yayin da ya tafi gidan karuwai a unguwar Aliyu Jodi a birnin Sokoto, The Punch ta ruwaito.
Galadima, mai shekaru 40, ya dade jami'an tsaro na nemansa ruwa a jallo, kimanin shekaru biyu, kuma ya kware wurin bawa masu garkuwa da yan bindiga bayani game da wadanda za su sace.
Premium Times ta ruwaito cewa da farko a jihar Niger Galadima ya ke sai daga baya ya koma jihar Sokoto inda aka damke shi.
Kakakin NSCDC, Shola Odumosu, ya ce an kama wanda ake zargin ne sakamakon bayannan sirri da jami'an NSCDC na Sokoto suka samu.
Shugaban NSCDC ya jinjinawa jami'an bisa nasarar kama Galadima
A wata sanarwar da ya fitar, kwamandan NSCDC na kasa, Dr Ahmed Audi ya yabawa rundunar ta jihar Sokoto bisa wannan nasarar.
Sanarwar ta ce:
"Dr Ahmed Audi ya yabawa NSCDC reshen jihar Sokoto bisa kama wanda ake zargin dan bindiga ne, Bello Galadima, mai shekaru 40 da aka shafe fiye da shekaru biyu ana nemansa ruwa a jallo.
"Galadima ya kware wurin harka da msu garkuwa yana basu bayanai game da wadanda za su sace. Yana kuma taimakawa masu garkuwa wurin siyo kwayoyi da wasu abubuwan da suka aikata laifi da su.
"An yi nasarar kama shi ne sakamakon bayannan sirri da jami'an NSCDC na jihar Sokoto suka samu inda nan take kafa masa tarko a unguwa Aliyu Jodi na Sokoto inda ya ke zuwa ya siya kwayoyi ya kuma shakata da karuwansa. Da haka ne jami'an suka cafke shi."
Odumosu ya yi bayanin cewa Galadima yana amsa tambayoyi sannan yana bada bayanai masu muhimmanci domin a kamo wasu.
A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa
A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.
Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.
Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.
Asali: Legit.ng