'Yan Bindiga Sun Tare Babban Hanyan Sokoto Zuwa Gusau, Sun Sace Motocci 3 Maƙil Da Matafiya

'Yan Bindiga Sun Tare Babban Hanyan Sokoto Zuwa Gusau, Sun Sace Motocci 3 Maƙil Da Matafiya

  • Yan bindiga sun sace fasinjoji cike da motoccin haya uku a hanyar Sokoto zuwa Gusau
  • Wani daga cikin direbobin da suka tsallake rijiya da baya ya magantu kan yadda lamarin ya kasance
  • Direban ya kuma yi kira da mahukunta da abin ya rataya a kansu da su yi gaggawar samar da tsaro a hanyar

'Yan fashin daji a ranar Lahadi sun tare hanyar Sokoto zuwa Gusau sun sace fasinjoji da ke cikin motoccin bus guda uku mallakar hukumar sufuri ta jihar Sokoto, rahoton The Punch.

Wani mai mota, Alhaji Mohammed Yusuf, da ya tsallake rijiya da baya yayin harin, ya shaidawa The Punch cewa yan fashin sun tare hanyar ne kusa da Dogon Karfe misalin karfe 3 na rana suka sace dukkan fasinjojin da ke cikin motoccin uku.

'Yan Bindiga Sun Tare Babban Hanyan Sokoto Zuwa Gusau, Sun Sace Motocci 3 Maƙil Da Matafiya
Masu Garkuwa Sun Tare Babban Hanyan Sokoto Zuwa Gusau, Sun Sace Motocci 3 Maƙil Da Matafiya. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

A cewar Yusuf:

"Kwatsam yan bindigan suka fito daga wurin da suka boye sannan suka fara harbe-harbe a iska, hakan ya tilastawa motoccin tsayawa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sheke Mutum 2 Tare da Awon Gaba da Wasu Kusan 100 a Sokoto

"Sun sace dukkan fasinjojin da ke cikin motoccin uku mallakar hukumar sufuri ta jihar Sokoto har da direbobin."

Yusuf ya kara da cewa a yayin da yan bindigan suka shiga daji tare da wadanda suka sace, sauran masu motoccin, har da shi, sun wuce da sauri kada yan bindigan su dawo su sace su.

"Suna barin wurin, dukkan mu muka tuka motoccin mu da gudu muka bar wurin, domin muna tunanin za su iya dawowa su sace wasu daga cikin mu," ya kara da cewa.

Ya yi kira ga mahukunta su samar da isashen tsaro a hanyar domin a cewarsa, yan bindigan na sace mutane a kowane rana.

Yusuf ya kara da cewa:

"Ya bindigan suna sace mutane a kowanne rana a hayar nan. Ina kira da hukumomin da abin ya rataya a kansu da su dauki matakin gaggawa domin magance lamarin."

Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ba domin ba a iya samun sa a wayarsa ba.

Kara karanta wannan

Kisar Ƴan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu

'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel