Siyasar Najeriya
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintri ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar wanda ake ci gaba da gudanarwa a fadin kasar nan na jam'iyyar PDP.
‘Dan takarar Gwamnan Oyo ya amince da shan kayi tun kafin a fara zaben tsaida gwani. Dama ba kasafai aka saba ganin gwamna mai-ci ya sha kasa a irin haka ba.
Gabanin zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fice daga takarar da ya bayyana.
Bayan haka kuma, wani dan takaran, Shehu Sani, ya ce yana ci gaba da fafutukarsa ta fitowa takarar gwamna a jam’iyyar PDP yayin da wasu ke ci gaba da fita.
Wata babbar kotun jihar Gombe ta bayar da belin Bala Sani mai shekaru 47, wani dan kasuwa mazaunin Abuja da aka tsare bayan ya caccakar gwamnatin Gwamna Yahaya.
Shehu Sani ya ce wani dan takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kaduna ya yi nasarar kwato kimanin naira miliyan 100 da ya baiwa deleget din jam’iyyar PDP.
A daren yau ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gana da Mallam Mamman Daura, dan uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma shugaban mukarraban Aso Rock.
Ɗan takarar mataimakin Gwamna a jam’iyyar APC Alhaji Murtala Sule Garo ya musanta rahoton cewa ya fice daga jam’iyyarsu ta APC zuwa PDP ko NNPP mai kayan dadi.
Wasu a APC su na kukan ana yunkurin ba Goodluck Jonathan tikitin APC, suka ce Ba zai yiwu a tsaida masa Dr. Jonathan takara a zaben 2023 bayan kifar da PDP ba.
Siyasar Najeriya
Samu kari