Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara
- Wata kungiya ta attajirai 'yan kabilar Igbo mazauna jihar Legas ta bayyana shirinta na tabbatar da cewa wanda zai gaji shugaba Buhari ya fito daga kudu maso gabas
- Kungiyar, Umunna Lekki Association (ULA), ta ce za ta ba da tallafin kudi ga duk wata jam’iyya da ta zabi dan kabilar Igbo a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa
- Ikem Umeh-Ezeoke, shugaban kungiyar, ya ce shugabancin Ibo zai sauya kasar gaba daya tare da hada kan ‘yan kasa
VGC, Lagos – Kiraye-kiraye da ake yi na neman shugaban kabilar Ibo a 2023 ya dauki saon salo a ranar Litinin, 14 ga Satumba, yayin da kungiyar Umunna Lekki Association (ULA) ta lissafa wadanda ka iya zama 'yan takara daga jihohin kudu maso gabas biyar.
Jaridar Guardian ta rahoto cewa ULA, wacce ta kunshi matasa 'yan kasuwa daga kasar Igbo mazauna Lekki, Ikoyi, Banana Island, Victoria Garden City (VGC) da Victoria Island na jihar Legas, ta bayyana shirinta na tallafawa shugabancin Igbo da kudaden su.
Legit.ng ta tattaro cewa a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Ikem Umeh-Ezeoke, ULA ta fitar da jerin fitattun yan kabilar Igbo maza da mata wadanda za su iya juya arzikin kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa kungiyar ta bayyana aniyar ta da kuma shirinta na bayar da gudummawar kudade na biliyoyin nairori ga manyan jam’iyyun siyasa biyu, All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) idan sun zabi ‘yan kabilar Igbo don daga tutocinsu a zaben shugaban kasa na 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
'Yan kabilar Igbo da za su iya tsayawa takarar shugaban kasa 2023
Ga jerin sunayen 'yan takarar da za a iya tantancewa don neman shugabancin Igbo:
1. Ngozi Okonjo-Iweala
2. Enyinnaya Abaribe
3. Orji Uzor Kalu
4. Peter Obi
5. Charles Udeogaranya
6. Ben Obi
7. Henry Okolie-Aboh
8. Governor Dave Umahi
9. Ogbonnaya Onu
10. Anyim Pius Anyim
11. Geoffrey Onyema
12. Barth Nnaji
13. Nnia Nwodo Jnr
14. Ike Ekweremadu
15. Emeka Ihedioha
16. Rochas Okorocha
17. Kema Chikwe
18. Humphrey Anumudu
Shugabancin 2023: Jerin manyan 'yan PDP 3 da za su yi gasar neman tikitin Jam'iyyar
A gefe guda, mun ji cewa yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke karatowa, 'yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa sun fara hararar tikitin jam’iyyarsu domin zama yan takara.
Ga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai ikirarin cewa manyan sunaye za su sake fitowa kamar yadda aka yi a zaben 2019.
Wasu daga cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su fafata don neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP su ne Bukola Saraki, Atiku Abubakar, da Aminu Tambuwal, duk da cewa har yanzu ba su nuna sha’awarsu a takarar ba.
Asali: Legit.ng