Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC

Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC

  • Kungiyar gwamnonin kudu ta jadadda matsayarta na cewa lallai sai dai a mikawa yankin shugabancin kasar a 2023
  • Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ya ce duk jam'iyyar da ta tsayar da dan arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa ba za ta samu goyon bayan yan kudu ba
  • Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta tsayar da dan takarar arewa a matsayin shugaban kasa a 2023 na iya rasa goyon bayan mutanen kudu.

Akeredolu ya bayyana haka ne ranar Juma’a a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels da TheCable ke sa ido.

Kara karanta wannan

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC
Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A yayin da yake magana kan kudurin kungiyar gwamnonin kudancin kasar kan zabukan 2023 da kuma cewa dole ne a bai wa yankin kudu shugabancin kasa, Akeredolu, wanda shi ne shugaban kungiyar, ya ce hakan ta kasance ne domin a yi adalci da daidaito.

Ya yi ikirarin cewa lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan Arewa, ya kammala wa’adin sa na biyu a 2023, yakamata shugaban kasa ya fito daga Kudu, jaridar Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akeredolu ya ce:

“Akwai kusan jam’iyyun siyasa uku da ke cikin Kungiyar Gwamnonin Kudu, muna da All Progressives Grand Alliance, Peoples Democratic Party da All Progressives Congress. Dukkanmu mun cimma matsayar cewa dole ne shugaban ƙasar nan mai zuwa ya fito daga Kudu.
"A gare mu, mun kasance a matsaya ɗaya. Ita kungiyar ba ta siyasa bace. Na yi imanin cewa duk jam'iyyar da ta zabi wani daga Arewa za ta fuskanci dukkan yankin kudancin kasar domin ba za su goyi bayan ta ba.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

“Dole ya fito daga Kudu. Muna cewa lallai dole a samu abun da zan kira da karba-karba. Adalcin sa da daidaito da ke cikin sa shine abin da muke wa'azi. Idan shugaban kasa Buhari - ya yi shekara takwas a kan mulki, ba zai yiwu ya fito daga Arewa ba. Dole ne shugaba na gaba ya fito daga Kudu.”

Yayin da yake mayar da martani ga masu sukar da suka ce cancanta ya kamata a duba a zaɓen 2023, Akeredolu ya ce akwai ƙwararrun mutane a yankunan arewa da kudu.

2023: APC ta magantu kan rade-radin za ta bai wa Jonathan tikitin takara shugabancin kasa

A wani labarin, jam’iyyar APC ta ce ba ta tabbatar wa da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan tabbacin tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba, kamar yadda ake ta yadawa.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sakataren CECPC, John Akpanudoedehe ya bayyana hakan a wata takarda a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara

Ya ce komawar mutum jam’iyya ba ya bayar da tabbacin a bashi wani matsayin a jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel