Yanzu-Yanzu: Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya fice daga jam'iyyar PDP ya koma APC mai mulki a Nigeria
  • Fani-Kayode wanda ya yi kaurin suna wurin sukar gwamnatin APC ya ce ya sauya shekar ne saboda hadin kan kasa
  • Fani-Kayode ya kuma ce yana daga cikin wadanda suka taka muhimmin rawa wurin zawarcin gwamnonin PDP da suka dawo APC kuma zai cigaba da hakan

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kamar yadda kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tuna baya: A 2019, FFK ya ce gara ya sheka lahira da ya koma APC

Yanzu-Yanzu: Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC
Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Fani-Kayode ya ce Allah ne ya yi masa jagora ya koma jam'iyyar na APC.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun hallarci taron.

Na taka rawa wurin zawarcin gwamnonin PDP da suka dawo APC, FFK

A yayin da ya ke jawabi, Fani-Kayode ya ce ya taka muhimmiyar rawa wurin zawarcin gwamnonin jam'iyyar PDP da suka koma APC.

Tsohon kakakin kamfen din shugaban kasar na PDP, wanda ya ce yana daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar APC, ya kara cewa ya koma APC ne don hada kan kasar.

Fani-Kayode ya ce yana da abokai da jam'iyyu da dama kuma a halin yanzu yana zawarcin Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Enugu, Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo da Bala Mohammed na jihar Bauchi su shigo APC.

Kara karanta wannan

Lamba 10 mai rabawa: Shugabannin FIFA da CAF sun ziyarci Buhari a Villa

Sauya shekar na ministan na zuwa ne watanni bayan ya musanta cewa zai fice daga jam'iyyar PDP.

Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi, a watan Fabrairu ya yi ikirarin cewa Fani-Kayode ya koma jam'iyyar APC.

Amma a wancan lokacin, Fani-Kayode ya karyata batun inda ya ce yana nan daram-dam a jam'iyyar PDP.

Ku saurari cikaken rahoton ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel