Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu

Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu

  • Me niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin sabuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (NNPP) Barista Olusegun Bamgbose, ya mutu
  • Bamgbose ya mutu ne a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba, bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Babban daraktan FENRA, Kwamared Nelson Nnanna Nwafor ya tabbatar da mutuwar dan siyasan

Barista Olusegun Bamgbose, me niyyar takarar kujerar shugaban kasa na sabuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (NNPP) ya rasu.

Bamgbose wanda ya kasance jagoran kungiyar masu fafutukar neman shugabanci nagari (CAGG) ya rasu a ranar Juma'a, 17 ga watan Satumba, bayan gajeriyar rashin lafiya, Daily Post da PM News sun ruwaito.

Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu
Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu
Asali: UGC

Da take magana kan rasuwar dan siyasar, Gidauniyar FENRAD, ta bayyana shi a matsayin babban muryar lamuran shugabanci nagari da fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.

Babban daraktan FENRA, Kwamared Nelson Nnanna Nwafor, ya bayyana cewa Bamgbose a rayuwarsa bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen kula da gwamnatoci yayin da ya ba da gudummawa ga muhimman batutuwan gina kasa.

Kara karanta wannan

Gagarumin matsala ya fara yayin da majalisa ta yi barazanar kama wasu manyan nade-naden Buhari

Nwafor ya ce:

“Ta hanyar sa bakinsa da ayyukansa, gwamnati ta sassauta manufofi da yawa da ba sani ba. Mutumin kirki ne, mai aiki tuƙuru, ƙaunataccen miji, uba da aboki ga kowa.
Tawali'unsa, da yadda yake tafiyar da lamura ya sa mutane da yawa suka ƙaunace shi. A duk tsawon zaman sa a duniya, ya himmatu ga haɓakawa tare da kare muhalli, ɗan adam, da haƙƙin dimokiraɗiyya waɗanda suka yi daidai da manufofin FENRAD.
"Lallai mun yi baƙin ciki da wannan rashi kuma muna addu'a gaAllah, a cikin wannan mawuyacin lokaci, ya ba wa danginsa ƙarfin jure wannan babban rashi; Haka kuma muna yin addu’a ga abokansa, abokan aiki da waɗanda wannan rashi ya shafa.”

A wani labari na daban, gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta tsayar da dan takarar arewa a matsayin shugaban kasa a 2023 na iya rasa goyon bayan mutanen kudu.

Kara karanta wannan

Sarki a Arewacin Najeriya ya ce mata su karbi mulki a hannun Buhari a 2023 kawai

Akeredolu ya bayyana haka ne ranar Juma’a a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels da TheCable ke sa ido.

A yayin da yake magana kan kudurin kungiyar gwamnonin kudancin kasar kan zabukan 2023 da kuma cewa dole ne a bai wa yankin kudu shugabancin kasa, Akeredolu, wanda shi ne shugaban kungiyar, ya ce hakan ta kasance ne domin a yi adalci da daidaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng