Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Tsayawa Takara a 2023

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Tsayawa Takara a 2023

  • Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya musanta rahoton cewa yana shirin tsayawa takarar gwamna a 2023
  • Kakakin majalisar ya bayyana cewa gwamnan jihar Lagos na yanzun yana yin abinda ya dace ga al'umma
  • Ya kuma kara da cewa a halin yanzun ya maida hankali ne kan mukaminsa na shugaban majalisar wakilai

Abuja - Kakakin majalisar dokokin Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa zai nemi takarar gwamnan jihar Lagos a 2023, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kakakin majalisar yace tunanin neman kujera mai lamba ɗaya a jihar Lagos bai taɓa zuwa cikin zuciyarsa ba.

Gbajabiamila ya kara da cewa gwamnan Lagos mai ci, Babajide Sanwo-Olu, yana yin abinda ya dace ga al'ummar jihar duk da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

2023: Shin Tinubu zai gaji Buhari? Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila
Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Tsayawa Takara a 2023 Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Kakakin majalisar ya bayyana haka ne a wata fira da kafar watsa labarai ta Channels tv.

Yace fara tunanin neman wani mukami a babban zaɓen dake tafe tun yanzun zai iya hana shi gudanar da aikinsa yanda ya kamata.

Ina son maida hankali kan aikina - Gbajabiamila

A jawabinsa, kakakin majalisar yace:

"Ina da ayyuka a gabana yanzun, bana bukatar duk wani abu da zai ja hankali na. Na sanar da makusanta na cewa ina son maida hankali ne kan mukamina da aikina na yanzu."
"Bani da wani shirin zama gwamna, kuma gwamnan mu na yanzun yana aikin da ya kamata. Maganar cewa ba'a maimaita gwamna a baya, ba shi ke tabbatar da hakan zata cigaba da kasancewa ba."
"Gwamnan jihar Lagos na yanzun yana kokarin yin abinda ya dace duk kuwa da halin matsin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

Inason kafa tarihi a kujerar kakaki

Kakakin majalisar yace yana son nan gaba a rinka tuna cewa, wani ɗan majalisar wakilai da ya shugabanci majalisa, ya yi aiki tukuru wajen cigaban ƙasa.

A wani labarin kuma tsohon ministan sadarwa yace yan Najeriya na da damar hukunta duk wani shugaba da ya yi ba dai-dai ba.

Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana, ya shawarci yan Najeriya kan matakin da ya dace su ɗauka kan shugabannin da suka gaza.

Gana ya bayyana cewa yan Najeriya suna da wuka da nama a hannunsu wajen zaɓar wanda suke so ya jagorance su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel