Kakakin Majalisa Ya Rantsar da Sabon Ɗan Majalisar Jam'iyyar PDP a Kaduna

Kakakin Majalisa Ya Rantsar da Sabon Ɗan Majalisar Jam'iyyar PDP a Kaduna

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, ya bada rantsuwar kama aiki ga sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Gari
  • Honorabul Ali Baba ya zama ɗan majalisa ne biyo bayan zaɓen cike gurbi da ya gudana a mazabar Sabon Gari a watan Yuni
  • Majalisar Kaduna ta bayyana kujerar da babu kowa saboda kin halartar harkokin majalisa da tsohon mai wakiltar yankin ya yi

Kaduna - Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani, ya rantsar da sabon ɗan majalisa, Alhaji Usman Ali-Baba, na jam'iyyar PDP ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ali Baba shine sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari, a majalisar dokokin jihar Kaduna.

Legit.ng Hausa ta gano cewa sabon ɗan majalisan ya lashe zaɓen maye gurbi, wanda ya gudana ranar 20 ga watan Yuni, 2020 a faɗin mazaɓar Sabon Gari.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dan Majlisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Koma APC

Majalisa ta rantsar da sabon mamba
Kakakin Majalisa Ya Rantsar da Sabon Ɗan Majalisar Jam'iyyar PDP a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ida zaku iya tunawa an gudanar da zaɓen cike gurbin ne biyo bayan bayyana kujerar ɗan majalisan yankin da babu kowa da majalisar dokokin Ƙaduna ta yi a watan Afrilu.

Meyafaru da ɗan majalisa na farko?

Majalisa ta bayyana kujerar da babu kowa ne saboda gazawar tsohon ɗan majalisa mai wakilatar yankin, Aminu Shagali, wajen shiga harkokin majalisa har na tsawon kwanaki 360.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rantsar da shi, Ali Baba ya godewa Allah (SWT), kakakin majalisa, mambobin majalisa, da kuma jam'iyyar PDP.

Hakazalika ya godewa al'ummar mazaɓar Sabon Gari, bisa ganin cancantarsa da kuma amince masa ya wakilce su a majalisar dokokin jihar.

Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno

A wani labarin kuma Sojoji da Dama Sun Mutu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Yiwa Tawagar Sojojin Kwantan Bauna a Borno

Kara karanta wannan

Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata

Akalla sojoji 10 ne suka kwanta dama yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka wa jerin gwanon sojojin kwantan Bauna a Borno, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin suna kan hanyarsu daga Monguno zuwa Maiduguri yayin da yan ta'addan suka far musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel