Da Dumi-Dumi: Dan Majlisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Koma APC

Da Dumi-Dumi: Dan Majlisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Koma APC

  • Wani ɗan majalisar wakilan tarayya, Promise Chisom Dike, daga jihar Ribas ya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasikar sauya shekar ɗan majalisar a zaman yau Alhamis
  • Shugaban masu rinjaye, Ado Doguwa, yace akwai sauran mambobin PDP da zasu koma APC a mako mai zuwa

Abuja - Ɗan majalisar wakilai, dake wakiltar mazaɓar Tai/Eleme/Oyigbo ta jihar Ribas, Promise Chisom Dike, ya fice daga PDP, ya koma jam'iyyar APC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya bayyana sauya sheƙar Mista Dike a zauren majalisa, ranar Alahamis.

Dike ya zama ɗan majalisar wakilai na biyu da ya sauya sheka zuwa APC daga jihar Ribas, a majalisa ta tara.

Dan majalisa ya koma APC
Dan Majlisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Koma APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ephraim Nwuzi, Wanda yake wakiltar mazaɓar Etche/Omuma, shi ya fara komawa APC daga jihar a watan Oktoba, 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane dalili yasa ɗan majalisar ya koma APC?

Dike ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne na ƙauracewa PDP saboda "rarrabuwar kai da kuma rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa."

Sai dai lamarin baiwa yan PDP daɗi ba, inda Ossai Ossai, mamba a jam'iyyar PDP ya ƙalubalanci sauya shekar ɗan majalisar.

Ossai yace mista Dike bai bayyana shaidarsa cewa akwai rikici da yaƙi karewa a cikin jam'iyyar hamayya ta PDP ba.

Amma kakakin majalisar, Gbajabiamila, ya dakatar da korafin, inda yace kotu ce take da alhakin fayyace gaskiya.

Akwai sauran masu sauya sheka

Yan majalisun jam'iyyar APC sun yi farin ciki da haka yayin da shugaban masu rinjaye, Ado Doguwa, yace akwai sauran yan majalisun PDP da zasu dawo APC mako mai zuwa, kamar yadda the cable ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, ya faɗi dalilin da yasa shugaban EFCC ya yanke jiki ya faɗi

Da yake martani kan lamarin, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, ya alaƙanta faɗuwar da takurawa kai da kuma yawan aiki.

Ministan ya yi kira ga yan Najeriya su saka Bawa cikin addu'o'insu, ya bayyana cewa shugaban ya samu kulawar da ta dace kuma ya dawo hayyacinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel