2023: APC da PDP na cikin sabon matsala, Ghali Na'Abba da Utomi na shirin bayyana sabuwar kungiyar siyasa
- Za a kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa, National Consultative Front (NCF) a ranar 1 ga watan Oktoba
- Yunusa Tanko, shugaban watsa labarai kuma daraktan hulda da jama'a na NCF, ya bayyana haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba
- Tanko ya bayyana cewa kungiyar ta rungumi wata jam'iyyar siyasa kuma tana aiki don sake fasalin ta don dacewa da ra’ayin ta
FCT, Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na iya fuskantar gagarumin hamayya a babban zaben 2023 kan shirin kaddamar da kungiyar tuntuba ta kasa (NCF) a ranar 1 ga Oktoba.
Legit.ng ta rahoto cewa NCF wata sabuwar kungiyar siyasa ce a shirye -shiryen babban zaben 2023.
A wata hira ta wayar tarho da jaridar The Punch, shugaban watsa labarai kuma daraktar harkokin jama’a na NCF, Dr. Yunusa Tanko, ya tabbatar da ci gaban a Abuja, a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.
Kungiyar ta kuma ce za ta yi amfani da wannan dama don tunawa da shugabanninta da suka mutu a wannan shekarar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, wasu daga cikin wadanda za a tuna da su sun hada da shugaban kwamitin ba da shawara na dattawan NCF, marigayi Dr. Ahmed Joda, marigayi Mallam Balarabe Musa, Innocent Chukwuma, Lady Rachel Oniga, da sauran su.
An tattaro cewa kungiyar ta rungumi wata jam'iyyar siyasa kuma tana aiki don sake fasalin ta don dacewa da manufarta na samar da sahihiyar madadin jam'iyyar All Progressives Congress da jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party.
Sanannen sanatan arewa ya fede biri har wutsiya kan mulkin karba-karba
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gaya wa wadanda ke kira ga mika shugabanci zuwa yankin kudancin ƙasar a 2023 da su binne tunaninsu.
An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin
Jaridar Punch ta rahoto cewa Adamu wanda shine sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma a majalisar tarayya ya bayyana mulkin karba-karba a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.
Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan na sau biyu ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng