Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna

Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna

  • Yanzu kallo ya koma sama yayin da yan siyasa ke shirye-shirye don samun tudun dafawa a babban zaben kasar na 2023 da ke kara gabatowa
  • Hasashe sun nuna cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yana hararar daya daga cikin muhimman kujeru biyu a babban zabe mai zuwa
  • Wadannan kujeru sune na mataimakin shugaban kasa ko kuma na dan majalisar dattawa

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yana auna tsare -tsaren ficewarsa da makomar siyasarsa bayan sauka a kujerar gwamna.

Ganduje ya fito fili ya ce ba shi da niyyar barin siyasa bayan ficewarsa daga gidan gwamnati, jaridar The Nation ta ruwaito.

Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna
Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna Hoto: Kano state government
Asali: UGC

Dan siyasar mai shekaru 71 ya ce zai ci gaba da yin siyasa bayan karewar wa'adin mulkinsa na biyu a 2023. Sai dai kuma, bai bayyana kai tsaye ko zai sake tsayawa takara ba ko a'a.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Ganduje, wanda ya shiga harkar siyasa tun 1978, ya ce idanunsa za su kasance a bude don amfanin kasa.

A lokacin da jaridar The Nation ta tambaye shi ko zai bi tafarkin takwaransa na jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda y ace zai bar siyasa a 2023 sai ya ce:

“Ban gaji ba ta koina; ba kuma zan yi murabus ko ritaya daga siyasa ba.”

Gwamnan yana lura da guguwar siyasa yayin da iskar ke kadawa. Makusantansa sun ce yana neman muhimman mukamai guda biyu yayin da yake duba hukuncin da jam’iyyarsa ta APC zata yanke.

Baya ga gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen gina jam’iyya mai mulki, Ganduje yana da kusanci da manyan jiga -jigan jam’iyyar APC da suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Haka kuma a lokuta daban -daban ya karbi bakuncin Muhammadu Buhari da jagoran jam'iyyar, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, inda aka ruwaito sun tattauna makomar jam'iyyar mai mulki.

Duk da haka, damar sa ta zama ɗan takarar shugaban ƙasa ya dogara da shawarar jam'iyyar.

Ba za a iya rinjayar tasirin Ganduje a babban zaben 2023 ba, idan aka yi la’akari da dimbin masu jefa ƙuri’a a Kano, wanda shine dalilin da ya ba Buhari nasara akan Goodluck Jonathan a 2015.

"Idan burinsa na zama mataimakin shugaban kasa bai yi nasara ba, Ganduje zai koma ga Majalisar Dattawa," in ji wani na kusa da shi.

Idan ya tsaya takarar Majalisar Dattawa, zai fuskanci wasu matsaloli ne kawai da zai tsallake.

Ya ce:

“Shugabancin jam’iyyar APC ya riga ya shirya mika masa tikitin takarar, idan yana da burin zama sanata, bayan haka, Sanata Barau Jibrin sanata mai ci wanda ke wakiltar gundumar Kano ta Arewa inda gwamnan ya fito, yana takarar gwamna.”

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

A wani labari na daban, akalla jagororin jam’iyyar APC 32 a jihar Taraba suna neman maye gurbin Saleh Mamman, wanda aka tsige daga mukamin Ministan wuta.

Jaridar Daily Trust tace manyan ‘yan siyasan Kano da Taraba inda Sabo Nanono da Injiniya Saleh Mamman suka fito, suna hangen kujerun Ministocin tarayya.

Ana sa rai shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tura sunayen wadanda za su maye guraben Ministocin da ya kora da zarar ‘yan majalisa sun dawo aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel