Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar Adawa PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar Adawa PDP Zuwa Jam'iyyar APC

  • Tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, Luka Barau Dameshi, ya fice daga PDP domin sake komawa tsohuwar jam'iyyarsa APC
  • Dameshi ya bayyana wa manema labarai cewa ya ɗauki wannan matakin ne a bisa karan kan shi
  • Ya yi aiki a matsayin mataimakin gwamnan Nasarawa lokacin zangon mulkin gwamna Tanko Al-makura na farko, daga shekarar 2011 zuwa 2015

Nasarawa - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Chief Luka Barau Dameshi, ya fice daga babbar jam'iyyar hamayya PDP, ya koma jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Dameshi, wanda ya bar APC a shekarar 2014 ya koma jam'iyyar PDP, ya bayyana matakin da ya ɗauka na sake komawa APC a wata wasika da ya aikewa shugaban jam'iyya.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa Ya Koma Jam'iyyar APC
Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar Adawa PDP Zuwa Jam'iyyar APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wasikar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba, ya saka adireshin shugaban PDP na gundumarsa, Ningo/Boher, ƙaramar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Labari Da Duminsa: Sanata Shehu Sani Ya Koma Jam'iyyar PDP

Meyasa ya fice daga PDP?

Da aka tuntuɓe shi domin bayyana dalilin sauya shekarsa daga PDP zuwa APC, tsohon mataimakin gwamnan ya amsa ta sakon karta kwana da cewa, "Eh na koma APC kuma a karan kaina na yanke hukunci."

Dameshi, ya yi aiki a matsayin mataimakin gwamnan jihar Nasarawa a lokacin zangon mulki na farko na gwamna Tanko Al-makura, daga shekarar 2011 zuwa 2015.

A wani labarin na daban kuma kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Zailani, ya rantsar da sabon ɗan majalisan jam'iyyar adawa PDP

Honorabul Ali Baba ya zama ɗan majalisa ne biyo bayan zaɓen cike gurbi da ya gudana a mazabar Sabon Gari a watan Yuni.

Majalisar Kaduna ta bayyana kujerar da babu kowa saboda kin halartar harkokin majalisa da tsohon mai wakiltar yankin ya yi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Dan Majlisar Tarayya Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP, Ya Koma APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262