Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC

Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC

  • Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babafemi Ojudu, ya yi martani a kan sauya shekar Femi Fani-Kayode daga PDP zuwa APC
  • Ojudu ya bayyana yau Alhamis a matsayin rana mafi muni a tarihin siyasarsa
  • A yau Alhamis, 16 ga watan Satumba ne dai Fani-Kayode wanda ya kasance babban dan adawar gwamnatin Buhari ya koma jam'iyya mai mulki a fadar shugaban kasa

Mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, bai ji dadi ba bayan Femi Fani-Kayode ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Hakan ya kasance ne yayin da ya bayyana ranar Alhamis a matsayin mafi muni a tarihin siyasarsa.

Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC
Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ojudu ya wallafa sakon a Facebook, sa'o'i kadan bayan FFK ya gana da maigidansa a Aso Rock sannan ya koma jam'iyyar da mai mulki.

Kara karanta wannan

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Ojudu ya wallafa:

"Wannan ita ce rana mafi muni a tarihin siyasata."

Daga baya Ojudu ya wallafa alwashin da FFK ya yi na cewa ba zai taba shiga APC ba, inda ya kara da cewa "Na gwammace mutuwa fiye da shiga APC".

Kafin ya koma APC, Fani-Kayode yana daya daga cikin fitattun yan adawa a kasar kuma ya kasance mai magana da yawun tsohuwar jam’iyyarsa a kamfen din neman shugabancin kasa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kamar yadda kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ya ce Allah ne ya yi masa jagora ya koma jam'iyyar na APC.

Kara karanta wannan

Tuna baya: A 2019, FFK ya ce gara ya sheka lahira da ya koma APC

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sun hallarci taron.

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

A gefe guda, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya sha alwashin tarkata gwamnonin jihohin Oyo, Bauchi da na Enugu zuwa jam'iyya mai mulki bayan komawarsa a yau.

Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da tsohon ministan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Fani-Kayode wanda ya zanta da manema labarai, ya ce lokaci yayi da ya dace ya hada kai da shugaban kasa wurin ciyar da Najeriya gaba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel