Siyasar Najeriya
Jam'iyyar PDP ta ce Kotun koli ta bai wa yan Najeriya kunya saboda ita kaɗai suke hange a matsayin gidan da zai musu adalci, ta ce hukuncin ya sab awa doka.
Shugaban ƙasa, Ahaji Muhammadu Buhari, ya ce hukuncin da Ƙoli ta yanke abin farin ciki ne gare shi da sauran yan Najeriya, ya ce lokaci ya yi da mutane zasu dara.
Babbar jam'iyyar adawa PDP ta ɗauki matakin dakatar da shugaban mata na jihar Ondo, Folorunso Makinde bisa zargin koƙarin lalata ragowar mutuncinta.
Jim kaɗan bayan yanke hukunci a Kotun Ƙolin Najeriya, an ga gwamnan Bayelsa, Douye Diri yana taya Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu a Villa.
Sanata Barau I. Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ya yi murna da hukuncin Kotun ƙoli, ya bukaci masu kara su maida wuƙarsu, su zo a haɗa kai a gina ƙasa.
Ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi su kira Shugaba Tinubu su taya shi murna.
Kotun ƙoli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoban 2023, ta yi watsi da buƙatar Atiku Abubakar ta shigar da sabbin hujjoji kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rigingimun jam'iyyar NNPP sun buɗe sabon babi yayin da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma suka amince da matakin korar Kwankwaso.
Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisun jiha da na tarayya ta tabbatar da nasarar Aminu Waziri Tambuwal a zaben Sanatan jihar Sakkwato ta kudu.
Siyasar Najeriya
Samu kari