Siyasar Najeriya
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya naɗa waɗanda za su jagoranci hukumomin NOSDRA da OORBDA, ya buƙaci su yi riko da gaskiya a ayyukan su.
Gabriel C. Onyendilefu, tsohon Akanta Janar a jihar Abia da kuma tsohon shugaban ƙaramar hukuma sun tattara bar jam'iyyar PDP, sun koma jam'iyyar APC.
Wata ƙungiya mai zaman kanta ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna ba sani ba sabo kan duk ministan da aka gano da gazawa a gwamnatinsa.
Yanzun nan aka sanar da wanda ya zama sabon sarkin Kano, inda aka bayyana Muhammadu Sanusi II ya zama sabon sarki a karo na biyu bayan shekaru a kasa.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa kasashen Mali, Niger da Burkina Faso da suka fice daga kungiyar ECOWAS a watan Janairu, suna kan hanayar dawowa.
Mamban majalisar dokokin jihar Kano ya ce da fushin sarakunan da Ganduje ya naɗa suka fara mulki kuma sun so rushe masarautun tun farkon rantsar da Abba Kabir.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma dan takara a jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa zai tsaya takara a 2027 da ke tafe.
Jami'an hukumar DSS da ƴan sanda sun kai ɗauki zauren majalisar dokokin jihar Kuros Ribas bayan ƴan majalisar sun tsige shugaba kan zargin almundahana.
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana abubuwan da ke kawowa mata cikas a siyasar Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari