Murna Yayin Da Tinubu Ya Naɗa Hadimar Buhari a Babban Muƙami, Bayanai Sun Fito

Murna Yayin Da Tinubu Ya Naɗa Hadimar Buhari a Babban Muƙami, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Didi Esther Walson-Jack a matsayin babbar sakatariyar ma'aikatar ilimi
  • Tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa ta a matsayin babbar sakatariya a ofishin shugaban ma'aikatan FG a 2017
  • Didi Esther ta kasance matar tsohon sakataren ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA kuma jagoran masu ilimantar da jama'a, Nimi Walson-Jack

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rabon muƙaman gwamnati da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ke yi a yan kwanakin nan ya dira Benin City, babban birnin jihar Edo.

A wannan karon, Shugaba Tinubu ya naɗa Didi Esther Walson-Jack a matsayin babbar sakatariya a ma'aikatar ilimi.

Shugaba Tinubu da Buhari.
Shugaba Tinubu Ya Nada Tsohuwar Hadimar Buhari a Ma'aikatar Ilimi Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Tsohon shugaban ƙasar da ya gabata, Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa matar a muƙamin gwamnati a shekarar 2017.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya rantsar da shugaban PDP a shirgegen muƙamin gwamnati, ya shiga taron FEC a Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta riƙe kujeru da dama a gwamnatin Buhari wanda ya haɗa da babbar sakatariya a ofishin shugabar ma'aikatan tarayya, ma'aikatar Neja Delta, ma'aikatar wuta da ruwa da tsaftar muhalli.

Takaitaccen bayani kan wadda Tinubu ya naɗa

A cewar Leadership, Esther Walson-Jack ta yi karatun firamare da sakandare a kwalejin mata ta gwamnatin tarayya da ke Benin da kuma makarantar gwamnati da ke Ilorin.

Ta kasance daga cikin ‘yan Najeriya na farko da suka yi karatu a makarantun hadin kan kasa (Unity Shools) haka kuma ta samu babban matsayi a ma’aikatar ilimi.

Esther Walson-Jack ta yi karatun shari’a a jami’ar Legas kuma an kira ta zuwa cikin tawagar lauyoyin Najeriya a 1987.

Ita ce uwar gidan tsohon babban sakataren kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) kuma jigo a fannin iliminantar da jama'a a Najeriya, Honorabul Nimi Walson-Jack.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar CCB? Gaskiya ta bayyana

Allah ya azurta waɗannan ma'auratan da samun 'ya'ya guda biyu wadanda kuma lauyoyi ne.

Tsohon hadimin gwamna ya fice PDP

A wani rahoton na daban Tsohon hadimin marigayi gwamnan jihar Ondo kan harkokin midiya, Allen Sawore ya fice daga jam'iyyar PDP.

Babban jigon siyasar ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda zaben gwamna na ƙaratowa kuma rikici ya yi yawa a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel