Siyasar Najeriya
Mai magana da yawun kungiyar haɗaka, Bolaji Abdullahi ya ce sun zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita saboda tsarinta da manufofinta.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon dan takarar gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar PDP, Ibrahim Ali Amin Little ya sanar da ficewa daga cikin jam'iyyar PDP.
Uban jam'iyyar ADC, Ralph Nwosu ya ce David Mark da Rauf Aregbesola suna da kwarewar jagorantar haɗakar ƴan adawa zuwa fadar shugaban kasa a zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya ce Najeriya ta lalace, inda ya zargi INEC da jam'iyyar APC (da ya ce 'ya'yanta barayi ne) da shirya murɗe zaɓuka masu zuwa. Ya koma ADC.
Amina Dogon-Yaro ta ajiye aiki a NTA don tsayawa takarar majalisar tarayya a mazabar Garki/Babura, inda ta samu goyon bayan jama'a don burin siyasar ta.
Yayin da ake ta kokarin haɗaka, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya fice daga APC yana cewa Najeriya ta lalace gaba ɗaya, kuma al'umma ba sa iya cin abinci.
Kakakin majalisar Filato ya yi murabus, an zaɓi Nanloong Daniel na APC, yayin da ake sa ran hakan zai dawo da zaman lafiya bayan rikicin siyasa a jihar.
Yayin da ake taron hadaka a Abuja, tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya fice daga jam’iyyar APC tare da shiga ADC, yana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali.
A kokarin hadakar jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Dino Melaye sun hallara a birnin Abuja domin kaddamar da jam'iyyar ADC a Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari