Siyasar Kano
Kungiyar Kwadago ta Najeriya watau NLC reshen jihar Kano ya bayyana goyon baya ga tazarcen gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP don ya yi tazarce a 2027.
An nada Munir Sanusi Bayero da Sanusi Ado Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano yayin da jami'an tsaro ke sintiri a harabar gidan sarauta a Galadanci.
Sakataren gwamnatin Kano da aka sauke, Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce zai fallasa cin hanci da rashawa a lokacin Abba Kabir. Ya ce da kyar Abba ya kai labari a 2027.
Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya karbi wasu 'yan APC da suka sauya sheka a gidan shi da ke Abuja. Kwankwaso ya gana da jakadan tarayyar Turai.
Wata kungiyar matasa ta daliban APC a jihar Kano ta ce komawar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba za ta amfani jam’iyyar ba, saboda rashin tasirinsa yanzu.
Tsagin NNPP ya zargi 'yan Kwankwasiyya da jawo ficewar Sanata Kawu Sumaila da wasu jiga jigan NNPP zuwa APC. Ya nemi a yi sulhu da Rabiu Kwankwaso.
Bayan gwamnan Delta ya shiga APC, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce wasu gwamnoni daga PDP za su sauya sheƙa zuwa cikinta kafin zaɓen 2027.
Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta nuna rashin damuwarta kan sauya shekar da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya yi zuwa APC mai adawa a jihar.
Tsohon kakakin majalisar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, wanda yanzu ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa APC.
Siyasar Kano
Samu kari