Shugaban Sojojin Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci jami'an tsaron Najeriya da su kawo karshen masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ke a fadin kasar nan.
Rundunar sojan saman Najeriya ta yi luguden wuta kan Boko Haram a Dutsen Mandara da ke jihar Borno. Ta wargaza wajen hada bom din yan ta'addar yayin harin.
An samu bambancin furuci tsakanin hukumomin tsaron kasar nan a kan harba bindiga yayin zanga-zangar lumana da matasan kasar nan ke gudanarwa saboda tsadar rayuwa.
Tsohon mai tsaron Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce ba mulkin soja da wasu yan Najeriya ke fata ne mafita ga wahalar rayuwa ba, ya bukaci a yi tunani.
Daga cikin matasa akalla guda biyar da iyalansu su ka tabbatar da rasuwarsu ta hanyar harbi yayin zanga-zanga, hudu daga cikinsu masu karancin shekaru ne.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa akasi aka samu har wani soja ya kashe yaro dan shekara 16 a garin Zariya. Rundunar ta ce ta cafke sojan a halin yanzu.
Rundunar sojan Najeriya ta caccaki masu ɓuya a rigar zanga-zanga tare da lalata wuraren ibada a tattakin da ke gudana na kwanaki 10 a fadin kasa.
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasa, Janar Christopher Musa, ya ja kunnen mutanen da ke daga tutar Rasha yayin zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar nan.
Sojoji sun tarwatsa mutane a wajen Mai shayi sun kwashe masa burodi da madara. Wani mazaunin unguwar Dorayi, Magaji Kabiru Getso ya yi wannan ikirari.
Shugaban Sojojin Najeriya
Samu kari