Ku Tuba Ku Mika Makamanku Tun Kafin Mu Karaso, COAS Yahaya Ga Yan Boko Haram/ISWAP

Ku Tuba Ku Mika Makamanku Tun Kafin Mu Karaso, COAS Yahaya Ga Yan Boko Haram/ISWAP

  • Shugaban sojojin ƙasan Najeriya, Manjo Farouk Yahaya, ya yi kira ga sauran yan ta'adda su mika makamansu
  • Yahaya ya yi wannan kira ne a Maiduguri yayin kaddamar da sabon shiri na musamman da zai kula da jin dadin sojoji
  • Yace duk waɗan da suka yi taurin kai suka ki mika makamansu to zasu haɗu da fushin sojoji

Borno - Shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya yi kira ga yan ta'adda su tuba tare da mika makamansu, kamar yadda the cable ta ruwaito.

COAS Yahaya ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a Maiduguri, jihar Borno yayin kaddamar da sabon shirin kula da jin dadin jami'an tsaro na haɗakar Operation Haɗin Kai.

Shugaban sojojin kasa, COAS Farouk Yahaya
Ku Tuba Ku Mika Makamanku Tun Kafin Mu Kariso, COAS Yahaya Ga Yan Boko Haram/ISWAP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yan ta'adda nawa suka mika wuya a hukumance?

A cewar rundunar sojojin kasa a makwanni biyu da suka shude sama da yan ta'adda 100 suka tuba tare da mika makamansu ga jami'an tsaro, kamar yadda punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwarazan Sojoji Sun Yi Gumurzu da Yan Boko Haram, Sun Ragargaje Su a Borno

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno tace zata cigaba da baiwa masu tada ƙayar bayan kwarin guiwa domin su mika wuya.

Wane mataki sojoji zasu ɗauka kan masu taurin kai?

Da yake jawabi a wurin taron manjo Yahaya yace duk waɗanda suka ki mika makamansu zasu fuskanci fushin sojoji domin zasu iso garesu.

COAS Yahaya yace:

"Muna samun nasara suna tuba da mika makamansu kuma muna kira gare su da su cigaba da aje makamansu domin su rungumi zaman lafiya."
"Muna kiran sauran dake can cikin daji su fito su mika makamansu saboda mu karkare wannan matsalolin."
"Amma idan suka yi taurin kai, to zamu isa gare su kamar yadda muka kai ga wasu, zamu shiga daji ga waɗanda suka yi taurin kai suka ki mika wuya ko a Arewa-Gabas ko Arewa-Yamma ko Arewa-Tsakiya."

Yahaya ya yaba da haɗin kan da ake samu tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro, inda ya kara da cewa ya fara haifar da ɗa mai ido.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

A wani labarin kuma Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaɗa kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni.

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel