Da Duminsa: Sojoji Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram Yayin da Suka Kai Hari Sun Hallaka da Dama a Borno

Da Duminsa: Sojoji Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram Yayin da Suka Kai Hari Sun Hallaka da Dama a Borno

  • Sojoji sun samu nasarar daƙile harin yan ta'addan Boko Haram a Ƙunmshe, jihar Borno
  • Kakakin sojin yace an yi gumurzu sosai tsakanin sojojin da yan ta'addan waɗanda suka zo da motocin yaƙi
  • COAS Farouk Yahaya, ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da jami'ansa suka yi, ya roƙe su kada su gaza

Rundunar sojin ƙasa ta sanar da cewa, a ranar Lahadi, jami'anta sun samu nasarar daƙile harin yan Boko Haram a garin Kumshe, jihar Borno, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Jirgin Yaƙin NAF Ya Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Yan Boko Haram da ISWAP a Borno

Kakakin sojin, Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar, yace zuwan jami'an soji yankin ne ya tilasta wa yan ta'addan tserewa ba tare da sun cimma kudirin su ba.

A jawabin nasa, kakakin sojin yace jami'an sun samu nasarar hallaƙa aƙalla yan Boko Haram shida yayin fafatawar.

Sojoji Sun Daƙile Harin Yan Boko Haram a Jihar Borno
Sojoji Sun Daƙile Harin Yan Boko Haram Sun Hallaka da Dama a Jihar Borno Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Yace: "Rundunar sojin operation haɗin kai a ranar Lahaɗi 20 ga watan Yuni sun daƙile harin da yan ta'addan Boko Haram suka yi niyyar kaiwa sansanin soji dake Ƙumshe."

"Yan ta'addan haye da motocin yaƙi 4 da mashina sun yi ƙoƙarin kai hari sansanin soji, amma sai suka haɗu da ruwan wuta daga gwarazan sojoji waɗanda suke a cikin shirin ko ta kwana, kuma nan take suka hallaka yan ta'adda 6."

"Sojojin basu gaza ba wajen fafatawa da yan Boko Haram ɗin, Hakan ya tilasta wa yan ta'addan tserewa ba shiri."

KARANTA ANAN: Sace Ɗalibai a Yauri: Sojoji Sun Sake Ragargazan Yan Bindiga Sun Kuɓutar da Malami da Wasu Dalibai

COAS Farouk Yahaya ya jinjina wa gwarazan sojojin

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya yabawa jami'an sojin bisa wannan juriya da suka yi har suka samu nasara.

Ya kuma roƙe su da su cigaba da nuna irin wannan juriya da namijin ƙoƙarin wajen tabbatar da an share duk wani ɗan ta'adda dake yankin.

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro Ta Sanya Gwamna Ya Kulle Wasu Makarantu a Jiharsa Saboda Sace Ɗalibai a Birnin Yauri

Gwamnatin jihar Kebbi ta bada umarnin kulle wasu makarantu a jihar guda baƙwai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ƙungiyar malaman makaranta, NUT, shine ya tabbatar da matakin gwamnatin ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel