'Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto, sun kashe sojoji biyu sun raunata 7, sun sace mutane da dabobi

'Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto, sun kashe sojoji biyu sun raunata 7, sun sace mutane da dabobi

  • Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Unguwar Lalle a ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sokoto
  • Yan bindigan sun kashe sojoji guda biyu sun kuma raunata wasu sojojin bakwai yayin harin
  • Majiyoyi daga ƙauyen sun ce ƴan bindiga sun iso garin kan babura kimanin 100 kowanne dauke da mutum 3 masu makamai

An kashe sojoji biyu an kuma jikkata wasu bakwai yayin harin da yan bindiga suka kai ƙauyen unguwar Lalle a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Daily Trust ta ruwaito.

Ƴan bindigan sun kuma ƙona motoccin sintiri biyu mallakar sojoji da ƴan sanda.

'Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto, sun kashe sojoji biyu sun raunata 7, sun sace mutane da dabobi
Dakarun Sojojin Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun kai hari ƙauyen ne misalin ƙarfe 2 na ranar Laraba.

Majiyoyi sun ce:

"Sun zo kan babura 100; kowacce babur dauke da mutum uku masu bindigu .

Kara karanta wannan

Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe

"Sun fito daga yankin Tilibale kuma suka bude wa sojojin da ke wani shinge a hanyar Sokoto zuwa Sabon Birni wuta.
"Sojojin sun mayar da martani amma yan bindigan suka yi galaba kansu saboda yawansu."

Mutane sun tsere daga kauyen bayan kai harin

Rahotanni sun ce motoccin sojoji guda uku sun bar Sabon Birni da sojoji amma aka tare su a hanya aka bindige sojoji biyu wasu bakwai suka samu rauni.

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Majiyar ya ce:

"A halin yanzu da na ke magana da kai, mutane sun watse daga Unguwar Lalle saboda tsoron wani hari."

Majiyar ta kara da cewa yan bindigan sun sace kayan masarufi daga shaguna, sun kuma sace dabbobi.

Yan bindigan sun kuma sace mutane da dama ciki har da ma'aikatan asibiti.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Mai magana da yawun sojoji Birgediya Janar Onyeoku ya ce ba a masa bayani game da lamarin ba.

Ba a samu ji ta bakin kakakin yan sanda, ASP Sanusi Abubakar ba domin ji ta bakinsa a lokacin hada wannan rahoton.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel