Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji

Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji

  • Hafsan sojin ƙasa, COAS Farouk Yahaya, ya umarci sojojin dake yaƙi da ta'addanci da cewa kada su sassauta
  • Manjo Yahaya ya faɗi hakane a wurin taron murnar zagayowar ranar sojojin Najeriya (NADCEL) 2021
  • COAS yace an samu nasarori da dama, amma bai kamata a sassauta ba har sai an gama ragargazar yan ta'adda

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya umarcin sojojin dake yaƙi da Boko Haram, ISWAP, yan bindiga sauran masu aikata ta'addanci da kada su sassauta har sai sun yi raga-raga da su baki ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana, Ta Faɗi Dalili

COAS ya bada wannan umarnin ne a sansanin soji dake Mogadishu, Abuja, yayin da ake gudanar da addu'o'i a coci a wurin taron murnar zagayowar ranar sojojin Najeriya 2021, kamar yadda the cable ta ruwaito.

COAS Farouk Yahaya
Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yace: "Ina roƙon kanmu baki ɗaya, kada mu sassauta a yakin da muke, mu cigaba har sai mun ci nasara, mun yi kaca-kaca da yan ta'adda baki ɗayansu a ƙasar mu. Mu dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

"Hakanan ina roƙon junan mu baki ɗaya, duk inda muka tsinci kanmu, mu kasance masu ɗaukar matakin da ya dace da kuma manufa."

"Idan muna da manufa kuma muka haɗa da addu'a to zamu isa inda muke buƙata"

"Mun samu nasarori da dama a yaƙin da muke, saboda haka bai kamata mu sassauta akan aikin mu ba, amma mu ɗora daga nasarorin da muka samu a baya." inji shi.

KARANTA ANAN: Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta Kan Wasu Yan Bindiga da Suka Kai Hari Caji Ofis

Najeriya na Alfahari da sojojinta

Daraktan gudanar da harkokin addinin kirista, Col. Islongo Mairiga, yayin da yake wa'azi, ya bayyana sojojin Najeriya a matsayin abun alfahari ga ƙasar.

Ya ƙara da cewa ya kamata sojojin su yi aiki tare da junansu domin samun nasara a kan dukkan maƙiyan zaman lafiya a ƙasa.

A wani labarin kuma Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da Fasto Tunde Bakare, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace Fasto Bakare, shine ya gabatar da shi ga shugaban ƙasa Buhari da jam'iyyar CPC a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262